Kaddara a Nahajul-balaga

Kaddara a Nahajul-balaga

Dalilai masu yawa ne muke da su a cikin addinin musulunci da suke nuna cewa dukkan wani abu yana da dalili, don haka masu fassara ma'anar kaddara da ma'anar da take kore samuwar hannun dan Adam a cikin ayyukansa da sakamakon ayyukansa sun kuskure hanya. Don haka ne muka ga ya kamata mu kawo wasu maganganu da suke nuna mana muhimmancin kaddara cikin ayyukan bayin Allah madaukaki.
Ga wadanda suka duba makalolin da muka rubuta kan hakikanin hukuncin Allah da kaddara zasu ga akwai bambanci tsakanin wannan da wadanda suka gabata, domin a wancan karon mun yi kokarin kawo dalilai ne masu muhimmanci kan ma’anar kaddara da hakikaninta, amma wannan karon muna son kawo bayaninta ne cikin wasu hikimomi na imam Ali (a.s), ta yadda zamu yi nuni da cewa kowane abu yana da sababi, don haka kaddara ba tana nufin cire rawar da ayyukan bayi suke takawa ba ne.
Wadannan ruwayoyi zasu taimaka mana wurin sanin hakan, idan mun duba wannan ruwayar da muka kawo da farko zamu ga tana nuna mana cewa, amsawa ta dogara bisa addu’a ne, samun gafara ya doru kan yin tuba ne, sannan samun dadin ni’imar Allah ya dogara bisa godiya ne.
Sai dai mu sani tuba, da godiya, da addu’a dukkaninsu akwai na zuci da suke bubbugowa daga zuciya da nufin dan Adam da kuma niyyarsa, wannan lamarin yana da muhimmanci matuka sosai. Sanna sai kuma na magana kamar karanta addu’a da fadin godiya ta tabbata ga Allah, da kalmar istigfari, sannan kuma sai na aiki ta yadda za a ga mai sabo ya yanke ya daina, mai neman gafara ya fuskanci yin ayyukan alheri, mai godiya kuwa yana kyautata wa al’umma da ni’imar da Allah ya ba shi.
Don haka idan Allah ya kaddara samun daya daga cikin wadannan abubuwan to yana kasancewa ya doru bisa samun motsi domin samun su daga ubangiji ne. Imam Ali (a.s) yana cewa: “Duk wanda aka ba wa hudu to ba za a haramta masa hudu ba : Duk wanda aka ba wa addu’a ba za a haramta masa amsa ba, kuma dukkan wanda aka ba wa tuba ba za a haramta masa karba ba, kuma duk wanda aka ba wa istigfari ba za a haramta masa gafara ba, kuma duk wanda aka ba wa godiya to ba za a haramta masa dadi ba. Kuma gaskiyar wannan a cikin littafin Allah shi ne fadin Allah madaukaki a cikin addu’a: Ku kira ni zan amsa muku, kuma ya fada game da istigfari: Duk wanda ya yi mummuna ko ya zalunci kansa sannan sai ya nemi gafarar Allah, zai samu Allah mai gafara mai rahama, haka nan ya fada game da godiya: Idan kun gode to zan kara muku. Ya fada game da tuba: Hakika tuba gun Allah na wadannan da suke aikata mummuna da jahilci ne, sannan sai su tuba a kusa, to wadannan Allah yana karban tubansu, kuma hakika Allah masani ne mai hikima". Hikima: 130.
Sannan an kaddara samun kariyar imani da yin sadaka, kamar yadda aka sanya kariyar dukiya da yin zakka. Don haka idan an kaddara kariyar wadannan abubuwan saboda mutane sun riko da abin da zai kare su ne, kamar yadda idan suka yi nesa da abin da zai kare su, sia su rasa kariya. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku kiyaye imaninku da sadaka, ku kare dukiyoyinku da zakka, ku kare tunkudowar bala’i da addu’a". Nahajul Balaga: Hikima: 138.
Don haka sababin komai yana doruwa bisa gareshi ne, idan mun duba ruwaya mai zuwa zamu ga hakan a fili cewa, da salla ake samun kusancin Allah ta yadda zamu iya cewa idan babu salla babu kusanci da Allah madaukaki. Imam Ali (a.s) ya ce: "Salla kusancin dukkan mai tsoron Allah ce, kuma hajji jihadin duk wani mai rauni ne, kuma kowane mutane yana da zakka, amma yin azumi ne zakkar jiki, kyakkyawan zaman aure kuma shi ne jihadin mace". Hikima: 131.
Haka nan idan mun duba alakar abota zamu ga cewa babu wani aboki da zai kiyaye amanar abokinsa sai idan yana da sharuddan yin hakan, don haka ne zamu ga Imam Ali (a.s) yana cewa: "Aboki ba ya zama aboki sai ya kiyaye abokinsa cikin abubuwa uku: Cikin bala'insa, da boyuwarsa, da mutuwarsa". Hikima: 129.
Idan muka ga aboki yana cin amanar abokinsa cikin wadannan abubuwan zamu ga abin da muke kira da kaddara cikin wannan lamarin tana nufin bai cika sharuddan kiyaye amanar abota ba, don haka ne ya ci amanar.
Idan mun duba abin da aka kaddara na arziki da yake saukowa ga bayin Allah, ko talauci da yake samun su, zamu ga dukkaninsu suna da kaddarawar Allah ta tun azal, amma duk da haka an sanya musu sabuban faruwarsu, muna iya nuni da wasu kalamai masu hikima daga Imam Ali (a.s) yayin da yake cewa:
"Ku nemi saukar arziki da yin sadaka, kuma duk wanda ya yi yakini da mayewa to zai kyautata bayarwa". Hikima: 132. Da kuma fadinsa: "Taimako yana sauka gwargwadon bukata ne". Hikima: 133.
Kamar yadda zamu ga yayin da ya fuskanci magana kan talauci sai ya kawo tsakaita rayuwa cikin sirrin abin da yake hana talauci. Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk mutumin da ya tsakaita a -rayuwa- ba zai yi talauci ba". Hikima: 134.
Sannan idan muka duba zamu ga wata magana mai matukar muhimmanci da take nuni da cewa; duk wanda ya karanta yawan ‘ya’ya da iyali zai kasance daya daga hanyoyin samun yalwarsa. Wannan lamari yana da muhimmanci matuka sabanin jahilcin da ya yadu a nahiyoyinmu na Afrika, ta yadda mutum zai kawo iyali da ‘ya’ya birjik da zimmar cewa zai bar wa Allah ciyar da su ba tare da ya dauki matakin kokarin samar musu da abin rayuwa ba.
A nan zamu ga wannan magana ta hikima da wasiyyin annabi (s.a.w) Imam Ali (a.s) yayin da yake cewa: "Karancin Iyali dayan Yalwa ne guda biyu, Soyayyar (mutane) rabin hankali ne, Bakin ciki rabin tsufa ne". Nahajul Balaga: Hikima: 135. A nan ne zamu fahimci cewa sai ka yi kiwo sannan sai ka ce Allah yana nan, wato Allah taya ni kiwo, ba Allah kiwata mini ba, don haka zamu fahimci bambanci tawakkali da Allah da kuma da saki sakaka.
Idan an kaddara musiba to an kaddara mata hakuri, kuma ba a ba wa mutum rashin jure shi ba matukar ya dogara da ruhinsa bai raunata shi ba, sai kaddara ta kasance tana zuwa gwargwadon saukar sharadinta ne. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Hakuri yana sauka ne gwargwadon musiba, wanda kuwa ya buga hannunsa a kan cinyarsa gun wata musiba, hakika ya shafe ladansa". Hikima: 131.
Hatta da ayyukan bayi an dora su bisa kaddara ne, idan ba a karba ba ko an karba duk ya doru bisa kaddara ne, domin idan sharudda sun cika za a karba, amma idan ba su cika ba babu batun karba. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Sau da yawa mai azumin da ba shi da komai a azuminsa sai kishirwa, kuma da yawa mai tsayuwar sallar dare ba shi da komai sai wahala, madalla da baccin masu hankali da cin abincinsu!". Hikima: 137. Sai imam Ali (a.s) ya ambaci cewa masu hankali su ne suke da sharuddan karbar ayyukan ibada.
A gurguje zamu yi nuni da wasu abubuwa masu muhimmanci wadanda suke doruwa kan wasu kamar haka: Sababin rabauta shi ne hakuri: Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai hakuri ba ya rasa rabauta ko da kuwa zamani ya tsawaita gareshi". Nahajul-balaga; Hikima:145.
Idan kuma aka kaddara wa wani tashi da wasu mutane mabarnata wadanda ba ya tare da su a ayyukansu, to saboda ya kasance ya yarda da ayyukan nasu ne. Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai yarda da aikin wasu mutane kamar mai shiga cikinsu ne tare da su, kuma duk wani mai shiga cikinsu yana da zunubi biyu: Zunubin aiki da shi, da zunubin yarda da shi" Nahajul-balaga; Hikima: 146.
Haka nan zamu ga cewa mallaka ita ce take jawo danniya ga abin mallaka, haka nan idan mutum ya yi takama da ra'ayinsa zai halaka, kuma idan mutum ya yi shawara da mazaje zai samu karuwa da ra'ayoyinsu, kuma ya amfana da su, haka nan wanda ya boye sirrinsa shi kadai ne zai yi abin da ya so da lamurransa. Duba fadin Imam Ali (a.s) game da wannan lamari yayin da yake cewa: "Wanda ya yi mallaka zai yi danniya, wanda ya kayatar da ra'ayinsa zai halaka, wanda ya yi shawara da mazaje zai yi  tarayya da su a  hankulansu, wanda kuma ya boye sirrinsa to zabin yana hannunsa". Nahajul-balaga; Hikima: 152. Don haka idan muka ce an kaddara sakamakon wadannan halaye ya samu mutum, to wannan sakamakon cewa yana da halayen ne.
Haka nan idan an kaddara wa wani rashin samun ci gaba kan wasu abubuwa zamu ga daya daga cikin dalilan haka shi ne yana da jin kansa, ta yadda yana nuna isa kana bin da ba shi da shi, kuma jiji da kansa yana hana shi neman karuwa. A Nahajul-balaga; Hikima: 157. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Jin kai yana hana neman daduwa".
Idan muka an kaddarawa wani cewa tunaninsa ya kawu, ta yadda ba ya tunani mai kyau, yana yi yana fadawa cikin dimuwa da raurawar tunani da rauninsa, daya daga cikin lamurran shi ne cewa yana gaba da wasu mutane bisa bangaranci ne ba bisa gaskiya ba, sau da yawa idan mutum yana kin mutane babu dalili na gaskiya, idan ya hadu da su yana magana da su kan lamarinsu ko yana tuhumarsu bisa karya sai tunaninsa ya samu rauni kamar yadda jikinsa yakan samu. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Gaba -don bangaranci ba gaskiya ba- tana kawar da tunani". Nahajul-balaga; Hikima: 169.
Wani lokaci mukan ga an kaddarawa wani kaskanci, ta yadda mutane suna wulakanta shi ko suna ganin rashin kimarsa, a nan ma zamu ga daya daga cikin dalilan haka shi ne kwadayi. Bahaushe yakan ce kwadayi babudin wahala, wato akan kaddara wa mai kwadayi hanyoyin wahala, sakamakon hanyar kwadayi da ya kama. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Kwadayi bauta ce madawwamiya". Nahajul-balaga; Hikima: 170.
Don haka kaddarar Allah ba haka nan kawai take zuwa ba, duk inda aka kaddara wani abu akwai dalilin da ya sanya hakan, ba kawai da ka, ko rashin tsari abubuwa suke wakana ba, Allah madaukaki mai hikima ne, ya fi karfin wasa da rashin tunani, bai yi tsari don wasa ba, tsarki ya tabbata gareshi.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Friday, May 21, 2010

 

Ƙara sabon ra'ayi