Tono Kabarin Hujru bn Udayyu

Malamai da sauran kungiyoyi na Musulunci da sauransu suna ci gaba da yin Allah wadai da harin ta'addancin da wasu 'yan ta'adda masu akidar kafirta al'ummar musulmi wato wahabiyawa salafawa na kasar suka kai hubbaren babban sahabin nan na Manzon Allah (s.a.w.a) wato Hijr bn Adi al-Kindi inda suka rusa hubbaren da tona kabarin nasa da kuma tafiya da gawarsa mai tsarki zuwa wani wajen da ba a tantance k ina ba ne.   A jiya Alhamis ne dai daya daga cikin kungiyoyin 'yan ta'addan ta kasar Siriya suka sanar da kai hari kan kabarin sahabi Hijr bn Adi din da ke yankin Adra na kasar Siriya wanda ya ke karkashin mamayan dakarun Jaishul Hur na kasar Siriyan inda suka keta hurumin wannan sahabi mai girma.   Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon dai tana daga cikin kungiyoyi na farko-farko da suka fara yin Allah wadai da wannan danyen aikin. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bayyana cewar wannan danyen aikin yana nuni da irin tunani da kuma yanayin wadanda suka aikata wannan aikin ne da kuma tabbatar da rashin gaskiyar ikirarin da suke yi na kare ababe masu tsarki na addinin Musulunci ciki kuwa har da sahaban Manzon Allah (s.a.w.a).   Shi ma a nasa bangaren firayi ministan kasar Iraki Nuri Al-Maliki ya yi Allah wadai da wannan danyen aikin inda yace babbar manufar masu irin wannan aiki ita ce cutar da hadin kan musulmi da kuma rarraba kansu. Har ila yau malaman addini a kasashen Iran, Siriya da Iraki da sauransu sun yi kakkausar suka ga wannan danyen aiki da kuma kiran wadanda suke da hannu cikin abin da ke faruwa a kasar Siriya da su gaggauta kawo karshen irin goyon bayan da suke ba wa wadannan 'yan ta'adda.   Shi dai Hijr bn Adi shi da dan'uwansa Hani bn Adi sun kasance daga cikin musulmin da suka karbi Musulunci a hannun Ma'aiki sannan kuma ya rayu da Ma'aiki (s.a.w.a) duk da cewa na dan wani lokaci ne amma dai an shaide shi da tsoron Allah da kuma mika wuya ga dukkanin umurni da koyarwar Ma'aiki.   Bayan rasuwar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya kasance daga cikin zababbun sahabban Amirul Muminin Aliyu bn Abi Talib (a.s). Ya kasance tare da Imam Ali (a.s) a manyan yakukuwansa guda uku wato yakukuwan Siffin, Jamal da kuma Nahrawan inda ya taka gagarumar rawa wajen kiyaye tushen Musulunci da kuma halifancin al'ummar musulmi karkashin jagoran Imam Ali (a.s).   Bayan shahadar Amirul Muminin (a.s) da kuma darewa karagar mulkin musulmi da Mu'awiyya bn Abi Sufyan yayi bayan sulhun da suka yi da Imam Hasan (a.s), Hijr bn Adi da sauran mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) sun fuskanci tsananin gaske daga wajen mahukuntan lokacin. Tun a farko-farkon mulkin nasa dai Mu'awiyya ya so yayi amfani da daya daga cikin gwamnoninsa wajen kashe Hijr to amma abin ya ci tura saboda irin matsayin da ya ke da shi a idon al'umma.   Bayan shahadar Imam Hasan (a.s), Hijr bn Adi ya koma wajen Imam Husain (a.s) da kuma kin mika wuya ga bukatar masu mulki na wancan lokacin lamarin da ya kara sanya shi da sauran mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) musamman na garin Kufa cikin tsanani da matsin lamba daga wajen jami'an gwamnatin Mu'awiyan lamarin da ya sanya daga karshe dai bisa umurnin Mu'awiyyan aka kashe wannan babban bawan Allah kuma daya daga cikin sahabban Ma'aiki (s.a.w.a).   Wannan shahada ta Hijr dai ta yi gagarumin tasiri cikin zukatan musulmi a wancan lokacin da kuma kara irin kiyayya da kyamar masu mulki na wancan lokacin karkashin jagoranci Mu'awiyya, kamar yadda a halin yanzu al'ummar musulmin suke ci gaba da nuna fushi da bakin cikinsu ga wadannan 'yan ta'addan da suka tona kabarinsa da keta huruminsa.

Daga Radio Hausa / Tehran

Ƙara sabon ra'ayi