Musulunci da Kiristanci - 1

Tattaunawar Musulunci da Kiristanci - 1

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Musulunci addini ne na hankali, kuma a wurare masu yawan gaske ne Kur'ani mai daraja ya kira mutane zuwa ga yin tunani da sanya hankali. Don haka ne ma musulunci bai yarda da koyi da wani a cikin lamuran akida ba, sai dai ya hau kowane musulmi ya yi tunani da dogaro da dalili kan akidarsa.
Ruwayayi da suka zo daga Ahlul-baiti tsarkaka (a.s) sun yin nuni da cewa; Tunanin awa daya kawai ya fi ibadar shekaru 70, domin da tunani ne wasu sasanni masu fadi zasu sake bude wa ga mutum, tayiwu wanda yake da shekaru 70 a kan hanyar barna da bata da ya yi tunanin awa daya da bai fada cikin wannan barnar ba.
Kur’ani yana nuni da nadamar wadanda suka tsinki kansu cikin musibu a lahira suna cewa ne da mun kasance muna hankalta ko muna sauraro da ba mu kasance cikin mutanen wuta ba.
Don haka ne zamu ga cewa mafi yawan mutganen da suka fada cikin bata da sun tsaya sun saurari masu fadin gaskiya suka sanya hankalinsu da sun samu tsira daga fadawa cikin tarkon shedan, don haka ke nan tattaunawa da juna tsakanin masu addinai mabambanta da kafa dalili mai nisantar bangaranci shi ne abin da ya fi dacewa mu zaba.
Allah madaukaki yana fada cewa: “… su ne wadannan da suke saurarar zance sai su bi mafi kyawunsa, wadannan su ne Allah ya shiryar, wadannan su ne ma’abota hankula”.
Musulunci ya girmama sayyida maryam (a.s) da annabi Isa (a.s) kuma ita kadaice masu da ambaton sunanta ya zo a Kur'ani mai daraja, ta yadda sura guda ta kasance da sunanta ne, kamar yadda an yi magana kan annabi isa (a.s) a surori daban-daban cikin Kur'ani. Don haka idan da wani kirista zai musulunta, to girmamawar da yake yi wa annabi isa (a.s) babu wani raguwa da zata yi, sai dai ma kaunarsa da annabi isa da babarsa maryam (a.s) ta karu.
Musulunci yana ganin maryar (a.s) a matsayin wata samfur abar koyi ga kamalar mutum wacce dukkan matan duniya ya kamata su fuskanta don samun samfurin rayuwa. Koyarwar musulunci tana cewa Allah zai kafa wa mata masu alfasha da zina hujja da maryam ne (a.s) domin ba su fi ta kyawu ba. kuma ya koyar da cewa maryam (a.s) ba ta taba yin aure ba kafin ta haifi annabi isa (a.s). Don haka ta samu ciki da haihuwa ta hanyar ruhi mai tsarki ne.
Musulunci yana ganin tuhuma da kazafin da yahudawa suka yi wa sayyida maryam na samun alakar kusanci da wani namiji a matsayin fita daga musulunci, ya karfafa cewa maryam (a.s) mai tsarki ce, don haka danta ma mai tsarki ne babu wata alfasha da ta shafe shi. Sai ya shelata wa duniya cewa isa (a.s) bawa ne na Allah kuma ya zo duniya babu Uba sai Uwa, kuma shi kalmar Allah ne da ya jefa wa maryam (a.s), kuma ruhinsa ne da ya hura a cikinsa.
Halittar annabi isa (a.s) tana daga cikin kashi uku na nau’in halitta da Allah ya yi mutum yayin da ya halicci Adam (a.s) babu uwa da uba, Hauwa (a.s) babu uwa, isa (a.s) babu uba, sauran mutane kuwa da uba da uwa. Don haka halittar mutum ba uba ba ta iya zama dalili na ubangijintakarsa faufau. Allah ya yi halittu masu yawa ba su da uba kuma wannan bai zama dalili na kasancewarsu ubangiji ba.
Adam (a.s) ba uba ba uwa. Macijiyar Musa (a.s) daga sandarsa ba uwa ba uba. Taguwar annabi salihu ba uba ba uwa. Shin kasancewarsu marasa iyaye yana iya zama dalilin ubangijintak gare su? Don haka akwai halittu da yawa da ba su da uba ba su da uwa, kuma wannan bai zama dalilin ubangijintakarsu ba.
Hada da cewa halittarsu samar da ita aka yi, wato babu su a da can sai suka samu, shi kuma duk wani abu da babu shi a da can sai ya samu to fararre ne. Don haka Allah ne kawai azalalle wanda ba shi da farko ba shi da karshe, amma sauran halittu suna da farko suna da karshe.
Sannan yaya hankali zai iya gamusa da cewa 3 tana zama 1 ne da akasin hakan. Batun cewa Allah, ruhi mai tsarki, isa, dukkansu ubangiji ne shi ma ya saba wa hankali a fili. Domin yaya kuwa annabi isa (a.s) zai zama ubangiji alhalin haihuwarsa aka yi, kuma kiristanci yana imani da cewa an rataye shi ne ya kuma bar wannan duniyar.
Wannan wane ubangiji ne da ake haifarsa, ake soke shi a tsire shi, kuma yake bukatar taimakon ubangijinsa?! Wane ubangiji ne wannan da yake tasowa yana girma tun yana yaro, yana da makiyan da zasu iya kashe shi?! Wane ubangiji ne wannan da yake da uwa, da kakanni?! Shi Wannan wane ubangiji ne da ake rataye shi. Isa (a.s) shi mutum ne kamili zababben Allah (s.w.t) da ubangiji ya yi masa baiwarsa.
Da wannane zamu ga irin kimar da musulunci yake ba wa annabi isa (a.s) babu wani addini a doron kasa da yake ba shi ita, bai yarda da keta huruminsa da tuhumar sayyida maryam (a.s) da alfasha tare da Yusuf Najjar da ba shi sunan dan zina da yahudawa suka yi ba. Kuma bai yarda da shisshigi da wuce gona da iri da fitar da shi daga cikin bayin Allah masu daukakar daraja zuwa matsayin ubangijintaka da Kiristoci suka yi ba.
Sai musulunci ya kasance addini matsakaici da ba ya takaitawa da muzanta ko wulakanta matsayin annabi isa (a.s), kamar yadda ba ya wuce gona da iri da fitar da shi daga bayin Allah zuwa ubangijintaka.
Ba a yi wa annabi isa (a.s) adalci ba cikin abin da littafi mai tsarki ya jingina masa, abin takaici ne a samu littafin yana siffanta shi da ‘ya’yan da aka samu ta hanyar kusanci da muharramai. Ko kuma cewa shi yana daga cikin zuriyar ‘ya’yan Lut (a.s) da aka samu ta hanyar zina da muharramai wanda shi ma jafa’I ne ga wadannan annabawan Allah biyu da ‘ya’yan annabi Lut (a.s).
Kiristanci addini ne da ya samu makiya masu yawan gaske a tarihinsa da suka yi kokarin jirkita shi, kuma sun cimma nasarar yin haka a wasu wurare domin gurbata shi. Musulunci ma ya yi fama da irin wadannan mutane da suka yi kokarin jirkita shi, sai dai musulunci ya samu kariya ne da ahlul-baiti (a.s) da manzon Allah (s.a.w) ya bar mana su domin su kasance makoma da kariya daga karkata da bata. Wadannan ahlul-baiti su ne halifofi 12 da ya bari da ya ambaci cewa na farkonsu dan’uwansa Ali (a.s), na karshensu dansa Mahadi (a.s).
Ubangiji bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, kuma ba shi da tamka ko wani da yake da dangantaka da shi, dukkansu bayinsa ne madaukaki, wanda dukansu gare shi ne suke bauta. Amma annabi Isa (a.s) kamar yadda imam Ridha (a.s) yake tambayar wani malamin kirista yayin da ya yi furuci cewa annabi isa as yana yawan bauta sai ya tambaye shi ga wa yake bauta? Don haka ubangiji ba ya bauta sai dai a yi masa bauta. Annabi Isa (a.s) yana bauta yana salla, yana azumi, yana addu’a, don haka shi wani bawa ne daga bayin Allah madukaki.
Idan annabi Isa (a.s) ya kasance ubangiji ne to maryam (a.s) zata kasance babar ubangiji ke nan. Sai babanta ya kasance kakan ubangiji, danginta su kasance dangin ubangiji ken an, sai ya kasance salsalarsa ta tafi ken an har zuwa kan kakansa Adam (a.s) wanda Allah (s.w.t) ya barranta daga wannan barranta mai girma.
Don haka ne sai annabi Isa (a.s) ya kasance yana bukatar yin magana tun yana karami domin ya kore wa al’ummar duniya tambayoyi biyu da suke yawo a tunaninsu cewar? Yaya kuwa za a haifi mutum ba uba? Kuma daga baya tun da Allah ya san cewa za a dangata wa annabi Isa (a.s) ubangijintaka, sai maganarsa ta farko ta kasance shi ne “Ni bawan Allah ne”.
Sai wannan maganar tasa ta kasance Magana ce mai tseratar shi da barrantar da shi daga abin da ake danganta masa na cewa shi Allah ne. Kuma ta barrantar da babarsa ta cewa ta samu alaka da wani namiji ne kafin samun wannan dan. Ta kuma tsarkake annabi Isa (a.s) daga jingina masa samun haihuwa daga lalataccen tsatso.
Maganar annabi Isa (a.s) tana nuna mana darajar babarsa da kimarta yayin da Allah (s.w.t) ya ba ta da wanda yake da wannan darajar da samun da mai matsayi a wurin Allah madaukaki. Annabi Isa (a.s) Allah ya ba ni matsayin mai rike masa butar alwala a wannan duniya, ya tashe ni da shi a lahira ya kasance mutum ne mai kamalar karshe da matsayi mai girma da daraja a wrin Allah. Allah madaukaki ya yi masa.
Isa (a.s) yana cewa: “Ya sanya ni mai albarka duk inda nake… aminci ya tabbata gare ni ranar da aka haife ni, da ranar da zan mutu, da ranar da za a tashe ni rayayye”. Don haka tuhumar Yahudawa gare shi ba ta da wani asasi kuma barna ce lalatacciya ce, kamar yadda musulunci yana ganin ta a matsayin kafice wa Allah ne da fita daga imani da shi. Don haka maganar Isa (a.s) yana jariri tana da hikima sosai, kuma saboda haka ne annabawa ba su bukaci magana suna jarirai ba amma annabi Isa (a.s) ya bukaci hakan.

Laccar: Sheikh Bahrami

Tarjamar; Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation

Ƙara sabon ra'ayi