Iran da Masar

Dalibai daga jami'o'i daban-daban na birnin Tehran, sun kai ziyara ga shugaban ofishin diplomasiyyar kasar Masar a Iran a gidansa da ke Tehran, inda suka ba shi kyautuka na musamman da kuma furanni, hakan ya zo ne bayan farmakin da wasu masu zafin ra'ayi suka kai kan gidan shugaban ofishin diplomasiyyar Iran a kasar Masar da ke birnin Alkahira, inda suka yi ta jefa duwatsu da takalma a kan gidan nasa, bisa hujjar banbancin mazhaba.

Ƙara sabon ra'ayi