Tattaunawa 8

Tattaunawa Ta Takwas

Sau da yawa kana koma wa maganar mutlakat ne har yau, ina ganin kana bukatar sanin ilimin Usulul fikh kafin ka fahimci wasu bayanai, idan dai ba zaka iya ganewa ba to ka bar tattaunawa, kana magana ba ka san inda zaka sanya ta ba. Sau da yawa kana Magana kana bayar da fassara, ina ganin maganarmu ba kan Halifofi uku take ba, sai dai ban san me ya sanya ka nacewa kowane misali sai dai da halifofi uku.
Sannan ka shahara da ayyana wa Allah wadanda yake nufi a cikin Littafinsa: Ina ganin zai zama shisshigi idan muka ayyana wadanda ake nufi ba tare da wani haske daga Littafin Allah ko hadisi sahihi ba. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa da halifa na farko (kamar yadda ya zo a littafin muwatta'I Malik), bayan ya tambaye shi ya ki sheda masa da alheri a duniya ya tambayi Annabi (s.a.w) dalili. Annabi (s.a.w) ya amsa masa da cewa domin ban san abin da zaku yi bayana ba!
Sannan dogaronka da wannan domin kore ilimin Annabi (s.a.w) da gaibi ba a mahallinsa ba ne; kuma na ji dadi da na ga ka yi nuni da wannan ka'ida da na lurasshe ka "wa'inna au iyyakum la'ala hudan…" ina fatan ka lizimce ta, sai dai ba ka yi amfani da ita a mahallinta ba. Sannan bahasin ilimin gaibi yana da bukatar na sa zaman na musamman, don haka shigarsa yana bukatar bayanai masu yawa domin ka san mene ne muke cewa.
Sannan kana maimaita musun wilayar Imam Ali (a.s) alhalin ka kasa kawo mai musun wilayar Ali koda kuwa mutum daya ne, don haka wilayarsa hujja ce a kanka a gaban Allah a gobe kiyama. Amma amfani da mutlakat kana bukatar zama mai cikakken masaniya kan abin da nake cewa sannan sai ka yi ta kawo mutlakat. Sannan da’iman kana ayyana wa Allah madaukaki wadanda yake nufi a wadannan ayoyin ba tare da wani haske daga littafi mai daraja ba ko hadisi madaukaki.
Sannan musun da kake yi wa Umar saboda ya yi furuci da wilayar Imam Ali (a.s) wannan ya nuna cewa ka yarda da cewa kana bin inda ya yi maka dadi ne a addini, domin Umar ya fada ka karyata, amma inda ya yi maka dadi sai ka yarda, addini ba haka yake ba, addini hujja ce. Koda yake kana iya bin duk abin da ka so.
Sannan tawilin da kake yi na sanya Imam Ali (a.s) ya yi tarayya cikin wannan zaluncin saboda bai mayar mata da Fadak ba; Ba mu sani ba ko kalmar da kuke jingina wa Shi’a ta zagin sahabbai tana kanku ne. Domin wannan kiyasin da ka yi mu ba mu yarda da shi ba a cikin addini, hada da cewa mai kayan ta mutu, kuma da ya dawo da shi ga 'ya'yanta da gobe bayan mutuwarsa an kwace.
Musun kai kuka kabarin Annabi (s.a.w) da sauransu yana nunawa a fili cewa ka nisanta daga sanin addini domin addinin nan cike yake da misalan da wasu suka kai kuka ga wanin Allah. ‘Ya’yan Annabi Ya’kub sun kai masa kuka, sannan Manzon Allah ya kai wa Sayyida Hadiza kuka, Da akwai misalai da ba zasu kirgu ba! Sannan wannan wani abu ne mai zaman kansa da yake bukatar lokaci na musamman.
Amma da ka yi da'awar cewa ana amfani da littafin makiyan Abubakar ne ina son ka kawo su waye makiyansa da muka yi amfani da littafinsu, Buhari ne ko Muslim in ya so sai mu san matsayinka a Sunnaci. Sannan kana magana da zafi ba tare da hujja ba, wannan ba ya iya bayar da ma’ana, Amma ina ganin yana da kyau ka nisanci tattaunawa ta addini har sai ka san littattafan Ahlus Sunna tukun. Domin wannan maganar ta inganta gun mafi ingancin littattafan tarihinsu kamar yadda kake gani, kuma wallahi ba na tsammanin ka fi Ibn Kutaiba da Dabari son Abubakar, kai hatta da ni da ka yi wannan kagen na ina kin Abubakar ba na tsammanin zaka iya rantsuwa da Allah cewa ka fi ni sonsa.
Amma da kake mamakin sahabbai da sauran mutane suna gani aka ja Imam Ali (a.s) kuma aka doki 'yar manzon rahama (s.a.w) da sauran wulakanci da aka yi wa sayyida Zahara har kana mamakin hakan, kuma har kake kiran wannan da tatsuniya: Ina ganin ya kamata ka daina tattaunawa kan addini har sai ka san mas’alolinsa da kyau, domin wurare da yawa irin wadannan sun faru: kana ina Annabi ya bayar da umarni a hudaibiyya in banda shi da Ali babu wanda ya yi har sai da mutane suka ga kamar azaba ce zata sauko kuma ka duba rawar da wasu suka taka a gaban Annabi har ma da hana bin sa da gaya masa bakar magana, kai kun ruwaito cewa akwai wanda ya shake wuyan Annabi ya hana shi yin salla ga ibn Ubayyi. Kuma kai kana ina Annabi ya la’anci duk wanda ya tura karkashin Usama idan ba su tafi ba, amma suka yarda su dauki wannan la’anar. Kana ina manzon Allah ya nemi a ba shi abin da zai rubuta wasiyyarsa amma aka hana shi, kuma ya kori wadanda suka hana din kuma ba su sake haduwa da shi ba har ya rasu. Wannan fa duk a littattan da ka yi imani da su akwai shi, har kake mamakin don an yi wa aalayen Annabi wani abu a bayansa don wani bai taimaka musu ba. Gaya mini wanda ba kashe shi aka yi ba daga aalayen Muhammad (s.a.w).
Amma da kake nuna goyon bayanka ga wadanda suka ki biyayya ga gyaran da Imam Ali (a.s) ya so ya kawo bayan ya riki mulkin al'umma, ke nan kana nufin ka ce shi imam Ali wadannan mutanen sun fi shi ilimi ke nan, ko kuma kai ma ka yarda da ra’ayinsu na cewa sunnar Umar ta fi ta manzon Allah ke nan..
Ina ganin ya kamata Imam Ali (a.s) alal akalla ya ci darajar cewa shi ma sahabi ne a wurinka idan dai har kana girma sahabbai din, domin wannan maganarsa ce.
Kai manzon Allah ya dawo da mukamu Ibrahim daga inda jahiliyya suka canja masa wuri ya mayar da shi wurin da Annabi Ibrahim (a.s) ya sanya shi da umarnin Allah amma a lokacin halifa na biyu Umar dan Khaddabi sai ya dawo da shi inda jahiliyya suka ajiye shi. Allah yayi hisabi tsakanin ka Umar(RA) An yi wa Ali (a.s) magana ya sake ajiye shi wurin da Annabi (s.a.w) ya sanya shi amma ya ce yana gudun kada a dauki Ka'aba wasa.
Bahasinka yana nuna jahilci a ciki yayin da kakan yi fushi ka yi zagi babu dalili, kana kiran kanka Ahlussunna amma kana tsananin kin abin da Ahlussunna suka rubuta da kansu idan aka gaya maka.
Wannan lamarin ya faru, kuma duk da hujjojin Ahlussunna a wurinka ba hujja ba ce, wannan yana nuna ke nan bahasi da kai ba shi da amfani tun da ba ka yarda da dukkan abin da Ahlussunna suka rubuta ba. Amma domin ilmantarwa ka duba:
Tarihin Ya'akubi: j 2, shafi: 149, wannan ya faru a shekarar 17 Hijira. Da Suyudi a Tarihul Khulafa. Da: Dumairi a Kitabul Haiwan a Kalmar Diik. Da: Alkamil fit Tarih, Ibnul Asir: 2/ 537. Dabakat Ibn Sa'ad 3/ 204. Sharhu Nahajul Balaga: 3/ 113.
Sheikh Naja Atta’i yana mai kawowa yana mai kafa sheda da wadannan abubuwan da muka kawo maka na littattafai cewa: Umar ya canja mahallin Mukamu Ibrahim (a.s) ya dauke shi daga inda Annabi Ibrahim da Isma'il (a.s) da manzon Allah (s.a.w) suka sanya shi ya mayar da shi inda Jahiliyya suka sanya shi.
Sannan; kuma Ibn zubair ya dawo da shi inda manzon Allah ya sanya shi, amma kuwa Abdulmalik ya sake dawo da shi inda Umar ya mayar da shi wato wurin da jahiliyyar Kuraishawa suka sanya shi bayan mamayar ruwa da gyara Ka’aba.
Amma duk abin da ya fi ba ni mamaki da kai shi ne inda ka nuna ba ka son Umar soyayya ta gaskiya, domin duk inda ya yi magana idan ya nuna yana da waliyyi wato sayyidi Ali (a.s) sai in ga ka ki yarda da Umar, wannan yana nuna son karya ga Umar ko ma sahabbai, domin da kana son su da ka dauki maganganunsu.
Amma wannan ya sake nuna mini abin da na gaya maka shekarar da ta gabata har ya sanya na tsayar da tattaunawa da kai domin ba ta da amfani.
Inda ka yarda da maganar sahabbai da littattafan Ahlussunna da tattaunawa da kai ta yi amfani!
Amma kagen da ka yi na takura wa 'yan Sunna a Iran wannan karya ce da ka sharara, kuma ka sani hisabinta yana kanka in ba ka nemi yafewar Allah ba. Domin Afganinstan da su mutanenku aka hada kai aka kashe ma’aikatan embassy na Iran da ma muminai da yawa amma suka yi hakuri, sannan sai Allah ya gwara kan mutanenku da iyayen gidansu wadanda suka rene su wato; Amerikawa, kamar yadda ya yi muku a can da kuma a Iraki. A baya sun sanya mutanenku yakar Shi’a, amma yanzu Allah ya gwara kansu. Kuma yanzu haka wadanda aka sanya su kare Isra’ila na mutanenku a Labanon, su ma muna nan zaka ga babu wani abu da Amurka da Isra’ilan zata tsinana musu tun daga mutanenku larabawa har na Afghan. Wadannan mutanen suka yi amfani da mutanenku wurin karkakatar da hadin kan musulmi, idan suka ga sun gama yi musu aiki sai kuma su rusa su da kansu.
Babban misali kana iya ganin shi ga wanda kuke gwarzantawa: bayan Regan ya ba shi Nobel na shaidar wanda ya fi kowa kawo zaman lafiya a duniya, amma bayan shugaba biyu kacal sai ga Bush ya sanya shi babban dan Ta’adda!.
A nan Iran da Shi'a da Sunna duk suna wuri daya kuma suna ibadojinsu suna kaunar juna in banda wadanda makiyan musulunci suka hure wa kunnuwa bayan sun fita daga kasar su ne suke dawowa da fitina. Amma Allah yana son masu gaskiya da neman hadin kai. Waye ya kirkiro neman hadin kan musulmi a cikin wadannan shekarun 30 kuma yake ta neman ganin ya samu hadin kansu, har ma yake cewa; duk wanda yake tayar da fitinar Shi’a Sunna shi ba Shi’a ba ne, kuma ba Sunna ba ne. Sai imam Khomain!.
Amma batun hadisin ridda da ya zo a cikin Buhari ina jiran ka kawo da wa ake, tun da ka ce ka san su, kamar yadda ka saba ayyawa Allah wadanda ake nufi. In ganin yana da kyau ka yi wa kanka adalci, ka kawo me ake nufi, bai kamata ka kasa kawo su wa ake nufi ba, kuma ka sani addini yakan zo da dokoki ne, idan wadannan dokoki wani ya siffanta da su sai su hau kansa.
Amma batun kafa hujjar wasici ka sani na kawo maka hujja can baya sai ka duba ka koma ka sanya hankali zaka ga dalili kar! Amma abubuwan da kake fada ina ganin ciwon da kake da shi shi ne ka dauka cewa abin da ka sani ka yi imani da shi haka nan yake wurin Allah, na sauran kuma bata ne. kai ke da matsala da ka ba wa ilmini Allah fassararka ka gaya masa wadanda yake nufi kuma kake so ya kasance yadda kake fassarawa. Don haka ne ba zaka iya fahimtar abin ta mahangar ilimi ba sai dai ta mahangarka.
Amma da kake cewa sharuddan umarni da kyakkyawa shi ne; dole ne duk sadda ka ga abin da ba daidai ba in har zaka iya kokarin gyara, to dole ne ka yi: Matsalarka shi ne ba ka san mafi yawan abin da yake munkarin ba, kuma ba ka san sharuddan yin sa ba. Don haka zaka yawaita yin kurakurai da su ma kuma munkari ne!. Saboda tayiwu kai kana ganin wani abu munkari alhalin ba munkarin ba ne!.
Ka sani umarni da kyakkyawa yana da sharudda idan sharudda suka fadi to ya saraya inda suka fadin. Ka duba yadda ka fada kana mai dogaro da hankali cewa shi ne dole ne duk sadda ka ga abin da ba daidai ba in har zaka iya kokarin gyara, to dole ne ka yi. Wannan ya sanya na gaya maka ba ka san sharuddan ba, don wannan ba sharadin ba ne!.
Amma maganar khairu ummatin da kake maimaitawa ka sani a littattafan da ka yi imani da su: Kun ce ku ne zaku zama shaida kan mutane ba ku yi zamani da su ba, sannan kana mamakin Annabi (s.a.w) zai yi shaida kan wasiyyansa bai yi zamani da su ba. Ka ga a nan ke nan har kun dara Annabi sanin halin mutane da abin da suka yi a duniya, wal'iyazu bil-Lah! Wannan a fahimtarka ma ken an ba ku yi adalci ga ilimin Annabi (s.a.w) ba.
Balle kuma lamarin ba yadda ka fahimta ba ne, Wannan ita ce matsalarka, koda yaushe kana fassara da yadda yake a kwakwalwarka ne. Wallahi khairu ummatin su ne Alayen Annabi (s.aw) kamar yadda ya gabata (a.s).
Ina ganin ya kamata ka dakatar da tattaunawa har sai ka yadda da cewa hujja tana iya hawa kanka ko kana so ko ba ka so matukar ta futo daga abin da ka yi imani da shi cewa ingantacce ne, in ba haka ba babu wani amfani ga tattaunawa.
Kada ka damu da wani kamar yadda wani bai damu da kai ba, ina ganin kowa ya yi nasa, idan wani abu ya hada mu kamar masallaci daya sai mu yi salla, kowa ya girmama abin da dayansa ya yi imani da shi ba tare da jahiltar juna ba.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Haidar Center For Islamic Propagation
Kammala gyarawa: July 1, 2009

Ƙara sabon ra'ayi