Tattaunawa 7
Tattaunawa Ta Bakwai
Ka nemi ci gaba da bahasin nan amma ina ganin kowa ya yi tasa fahimtar ya fi kyau, sa'an nan mu kaunaci juna kan abin da muka hadu, mu girmama juna kan abin da muka rabu.
Amma da kake son sanin matsayin wadanda suka ki biyayya ga Ali (a.s) sai na ce maka: Hukuncin wurin Allah koda kuwa wani ya yi hasashe yana iya zama kuskure domin wannan wani abu ne da yake a hannun Allah kawai.
Amma musulmin duniya kowa yana da nasa ra'ayi a kan hakan, domin akwai wanda ya hana a ma koma baya a kalli wannan kuskure da ya faru da ya hada da barin wasiyyar Annabi (s.a.w) kan wanda zai gaje shi a tafiyar da lamurran al'umma bayansa, don haka ne ma wasu suka yi kokarin toshe wannan kuren da cewa; ba a ma yi wasiyya ba duk da lamarin wasiyya da Littafin Allah da Alayen Annabi (s.a.w) wani abu ne mutawatiri. Sa'an nan ga lamarin kwacewa 'yar manzon Allah gonarta da manzon Allah ya ba ta wacce aka fi sani da Fadak wadda hatta da asbabun nuzul na Suyudi da littattafai da yawa sun yi magana kan yadda manzon Allah ya ba ta Fadak, da yi mata bulala, da kuma mafi muni shi ne dukanta da yin sanadin barin cikin danta Muhsin da kuma fasa kyauren gidanta da ya jawo huda kirjinta da fasa shi da kusoshi biyu wanda ya yi sanadin rayuwarta har ta yi fushi da al'ummar musulmi gaba daya ta nemi a boye kabarinta kada kowa ya sani domin kawai ta nuna fushinta da wannan al'umma, har ma Buhari ya kawo maganganunta masu zafi kan halifofin farko da suka gabaci mijinta Imam Ali (a.s) saboda sha'anin da ya faru na jagorancin al'umma bayan Annabi (s.a.w). Wannan ne ma ya sanya aka samu kowa yana kallon abin ta mahangarsa da da ra'ayoyi iri-iri daban-daban daidai gwargwadon fahimtar kowannensu.
Sai aka kasu gidaje mabanbanta, kowa yana da nasa ra'ayi, sai masu bin koyarwar Banu Umayya da malamansu suka tafi a kan farin ciki da wannan lamari, wani abin mamaki shi ne yin biki da ranar da aka kashe danta wato; Imam Husain (a.s), kwanan nan ne wasu littattafai suke dada karfafa jin dadin abin da ya faru na kashe shi suna masu nuni da gwara haka! kai suna cewa ma laifinsa ne!! wal'iyazu bil-Lah!.
Lamarin sanin matsayin wadanda suka yi watsi da wasiyyar Annabi (s.a.w) lallai lamari ne mai wuyar sha'ani da ya sanya gaba mai tsanani tsakanin musulmi, har ma na kai ga natijar cewa duk wanda ya yi bincike ya samu abin da yake ganin shi ne zai zame masa uzuri har ga Allah to sai ya yi aiki da wannan ya kyale sauran masu ra'ayoyi kowa ya je da nasa in ya so ranar lahira sai Allah ya yi wa kowa hisabi da abin da yake gani maslaha ga kowane bawa daidai yadda ya yi ikhlasi ya cimma gaskiya ba son zuciyarsa a ciki.
Mafi yawancin masu bayani sun kawo wannan canjin a matsayin abin da ya haifar da musibu sakamakon kauce wa Ahlul Baiti (a.s) da ya sanya komai ya jirkice kuma sun fassara wannan lamarin yana cikin irin matsayoyi da Annabi ya yi nuni da shi mai tsanani kan sahabbansa a hadisan nan da Buhari da Muslim da Ahmad da sauran manyan malaman hadisi suka ruwaito kamar haka: Muslim: 4/1793. Buhari: 28/26. Masnad Ahmad: 1/ 253, 258.
A cikin akwai hadisan da suka yi nuni da za a yi wuta da sahabbai sai ka duba, har ma manzon Allah ya ki yarda sai a ce masa ba ka san abin da suka yi bayanka ba. A wasu ruwayoyin sun yi ridda bayanka. Sannan Abuddarda' da Anas dan Malik sun yi furuci tun a zamaninsu da babu wani abu da ake yi lokacin manzon Allah (s.a.w) sai da aka canja shi!
Hada da abin da manzon Allah (s.a.w) ya gaya wa halifa na farko kamar yadda ya zo a cikin littafin nan na Muwadda'r Malik cewa; Ba zai nema masa gafara ba domin bai san abin da zasu yi ba a bayansa. Kuma wannan lamari na matakin da Annabi ya fada a hadisai madaukaka su ne abin da wasu manyan sahabbai masu daraja kamar su Salman Farisi da Ammar da Bilal suke a kai; sai dai ni bayan bincike da ya dade tare da malamaina na tafi a kan cewa; Wannan lamari ne mai wuyar sha'ani kuma ina ganin wadanda suka yi hakan na saba wa wasiyyar Annabi (s.a.w) da hayewa karagar jagoranci: sun yi ijitihadi ne suka yi kuskure, ba kamar yadda wasu suke ganin sun yi haka ne da gangan domin kwadayin mulki ko kuma neman rusa musulunci. Abu guda ne ba zamu iya korewa ba shi ne akwai kuskure a kan abin da ya faru.
Amma matsayin wadanda basu koyi (takalidanci) da maganganun Ahlul Baiti?: Wannan ma matsayinsu yana koma wa ga Allah madaukaki ne, kuma shi ne zai saka wa kowa da abin da ya yi daidai gwargwadon ikhlasinsa da tsarkin niyya. Domin haka ne kowa sai ya yi sa'ayi "Inna sa'ayakum lashatta.. da ayoyin da suka biyo bayanta.
Sai kowa ya koma ya yi binciken wasiyyar Annabi (s.a.w) da cewa me ya yi wa al'umma wasici da shi, kuma shin al'umma ta kiyaye ko kuwa? Waye ya ce a yi biyayya gareshi bayansa domin ya binciki me ya ce domin ya samu uzurin yin addini daidai a wurin Allah madaukaki? da sauran tambayoyi masu yawa da suke cikin kwakwalenmu.
Da fatan zaka bar ni haka nan domin ba ni da lokacin wadannan bahasosi sosai musamman a wadannan lokuta, wadannan bahasoshi ne da suka gajiyar da musulmi, ina ganin lokaci ya yi da kowa zai kiyaye kimar abin da kowa yake a kai ba tare da ya yi suka ko isgili da abin da wani yake girmamawa ba, kai komai kimar mutum yanzu a wurina idan ya yi suka ga wani ra'ayi ko isgili to da ni da shi mun raba gida, don haka ina ganin ka dage da bincike idan ka kai ga natija kowace iri ce har a zuciyarka to ka yi tsarkin niyya a kanta ka bi ta, amma ka kuma shirya wa amsar da zaka ba wa Ubangijinka a ranar lahira bias abin da ka gamsu a kansa. Allah ya sa mu dace.
Game da amsarka ta ba dole ba ne saninka, sai in ce: Babu damuwa, duk inda muke abin nema ita ce yardar Allah, amma ganin kamar ka damu da wadannan bahasosi ne, wadanda suke nuna kyakkyawar niyyarka ta neman sanin makomarka da kuma ikhlasinka na ganin an yi addini da hujja kamar yadda yake tun farko daga ma'aikin Allah ne ya sanya na ga bari in hada ka da wani domin ku yi ta yin bahasi, amma idan ba haka ba ban taba tambayarka wannan ba.
Kada ka damu da ganin mutane sun bace ko sun kauce wa hanya wannan abu ne wanda na zauna cikinsa ni ma kusan shekaru sama da goma amma daga baya na cimma natijar cewa; idan duk duniya zasu koma kafirci to bai kamata mutum ya damu kansa ba kuma wannan ne umarnin Allah ga annabinsa, sai dai kowa ya tsaya gun haddin nasa kada ya taba na wani, wannan shi ne kawai zai sanya kowa ya koma bincike da kuma samun zaman lafiya tsakanin al'Ummu gaba daya, kuma wannan ne musulunci ya zo da shi daga wanda ya fi kowa kishinmu fiye da kawukanmu. Kada ka manta cewa; ba yadda za a yi mutane su koma yadda kake so, domin Allah ma bai yi su domin ya gan su yadda yake so ba, sai dai shi zai kama kowa da kaucewarsa ne bayan ya dora musu hujja da aiko manzanni da isar da sako.
Amma dagewarka a kan sai ka ci gaba da wannan bahasin ina ganin ba ka son ka bar wannan bahasi, ka sani ya kamata ne kowa ya riki abin da ya yi yakini da shi ba tare da samun damuwa da na wani ba, sannan duk wanda ka gamsu da shi daidai hakan ne Allah zai yi maka hisabi. Sannan ni a wannan kwanakin ina da karancin lokaci matuka da gaske don yin wadannan bahasosi, don haka ne ma nakan dan jima wani lokaci ban koma wa email ba.
Amma ayoyin da kake kawo wa domin nuna ismar sahabbai da cewa ba sa sabo ko kuma dole dukkaninsu daya ne makomarsu daya, Ayoyi ne da ka kawo masu nuna cewa akwai itlaki a cikinsu, don haka Allah madaukaki mai hikima ya kawo musu kaidoji kamar: "waman nakasa fa'innama yankusu ala nafsih" da "wamimman haulakun minal a'arabi…" da "izaja'akal munafikuna…" da "…in kalabatum ala a'akabikum, faman yankalib…" da "faman nakasa fa'innama yankusu ala nafsihi…" da "…wa'adallahul lazina amanu minhum…". Hatta da irinsu "hazani hashamani…" a karshenta akwai kaidi da cewa; "fallazina kafaru kutti'ata lahum siyabum minannar…".
Sannan da kake ayyana wadanda ake nufi ina ganin zai zama shisshigi idan muka ayyana wadanda ake nufi ba tare da wani haske daga Littafin Allah ko hadisi sahihi ba. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa da halifa na farko (kamar yadda ya zo a littafin muwatta'I Malik), bayan ya tambaye shi ya ki sheda masa da alheri a duniya ya tambayi Annabi (s.a.w) dalili. Annabi (s.a.w) ya amsa masa da cewa domin ban san abin da zaku yi bayana ba! Amma sai ga shi kana nuna wa Allah su wa yake nufi da wadannan ayoyi kana mai kawo sunaye. Ayoyin Kur'ani mai daraja mutlakai ba ka iya ayyana masadik dinsu a ka'ida sai ka dogara da shari'a. Kamar yadda manzon rahama da kansa ya nuna su waye; Ahlul Baiti (a.s) kuma ya nuna su waye nisa'ana, kuma ya nuna waye wallazina amanul lazina yukimunassalata…, da sauran wurare.
Ina ganin lokaci ya yi da zaka guji yin tafsiri da ra'ayi da ka so domin ya yi daidai da mazhabarka, ka nemi taimako daga hasken ruwayoyi sahihai, ka koma wa littafi da hadisai ingantattu tukun.
Na ji dadi da na ga ka yi nuni da wannan ka'ida da na lurasshe ka "wa'inna au iyyakum la'ala hudan…" ina fatan ka lizimce ta, sai dai ka yi amfani da ita a mahallinta.
Sannan da kake cewa; Kana ganin Allah zai yarda da mutum kuma yayi kuskure a sha'anin da Allah ya yadda da shi akai kana mai kawo ayoyi kamar haka: (wallazinattaba'uhum bi ihsanin radiyallahu anhum wa radu anhu) (Allazina in makkannahum fil ardi akamussalata wa atawuzzakata wa amaru bil ma'arufi wa nahau anil munkar...) da sauransu, sannan kuma daga karshen maganarka kana musun wilayar Ali (a.s), kana mai da'awar abin da babu shi; a yaushe ne malamai suka yi musun wilayar Imam Ali (a.s) a yaushe ne suka ce hadisan maudu'ai ne, a yaushe ne wannan ya faru alhalin Buhari da Muslim da ibn majah da Tirmiji da Ahmad da Hakim da sauran manyan maruwaita suna karfafa wilayar Imam Ali (a.s) kai ga ma sauran mafassara Kur'ani. Ga Umar dan Khaddabi yana furuci da wannan fifiko na Imam Ali (a.s) amma waye ya isa ya yi musun wannan daraja da daukak bayan Umar ya tabbatar da ita gareshi!
Ga shi a ranar Gadir Umar yana cewa da shi: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abi Dalib, hakika ka wayi gari kana shugabana kuma shugaban dukkan mumini da mumina. Ga wasu daga cikin wadannan masdarori da suka yi bayani game da Gadir karara da bayanai dalla-dalla da shelanta wilayar imam Ali da babu mai musu sai munafuki, da kuma murnar da Umar dan Khaddabi ya taya shi kamar haka:
Tarihu Bagdad: j 8, shafi: 20, alkahira. Sam'ani Naishaburi a Fadha'ilus sahaba: Da Baihaki: da sanadin da ya gabata. Da Allama Akhdab Khawarizimi: a Manakib, shafi: 93. Da Zakha'irul Ukuba: shafi: 67. Da Masnad: Ahmad bn Hambal. Da: Fara'idus Simdain. Da: Dabari. Da: sauransu.
A yanzu akwai wani daga cikinku da isa ya karyata Umar dan Khaddabi wanda shi ya fi ku sanin waye Ali (a.s)!! ko kuwa ba ku gaskata Umar ba sai inda ya yi muku dadi!!! Hada da abin da ya gabata gareka tun baya yayin da Umar ya yi furuci da cewa; bai'ar da aka yi wa Abubakar kuskure ce.
To idan wannan bai'ar kuskure ce; sannan kuma ta Umar dan Khaddabi ta dogara da wasiyyar wanda yake bai'arsa kuskure ce a fadinsa da bakinsa, sannan ta halifa na Uku ta dogara da wannan ta biyun, ke nan ka ga duk bai'ar ta doru bisa kuskure, wannan yana nufin ke nan sai a nemi wanda yi masa bai'a take sahihiya, kuma ba ka isa ba gabas da yamma ka samu wani wanda yake haka duk duniya sai Ali (a.s)!.
Kuma ina hada maka da kalubalen ka kawo wani malami madogara kwara daya rak da ya yi musun wilayar Imam Ali (a.s) in akwai! Kuma wannan bashi ne da ya hau kanka!
Ina iya kawo maka misali daya cikin daruruwa, duba abin da manzon Allah yake gaya wa khalid dan walid yayin da Manzo ya kwabe shi ya hana shi sukan Ali (a.s) yana mai gaya masa shi ne jagoranku bayana, da sauran ruwayoyi masu nuni da wannan:
Duba: Khasa'isun Nisa'i: 24. Da Haisami a Majma'uz Zawa'id: 9/ 127-128. Da Muntaki: a Kanzul Ummal: 6/ 154-155. da Zakha'irul Ukuba, daga Ahmad dan Hambal a manakib: 68. Da Dabarani a tarihinsa: 3/ 17. Da Mustadrak: 3/ 110. Da Sa'alabi a Tafsirinsa a sallar Isra'i. Da Arraudha: 11. Da akwai dubunnai dalilai sai dai tsoron tsawaitawa da karancin lokuta.
Sannan wahayi shi ne ya zo da biyayya ga manzon Allah bayan Ubangiji da kuma Ulul amri kuma Manzo ya yi bayanin su waye ulul amri, sannan Kur'ani ya yi nuni a sababin nuzulinsa da "Innma waliyyukumul Lahu…"; da ta yi nuni da Allah da Manzo (s.a.w) da Imam Ali (a.s): Arriyadhun Nadhira: 2/ 302. Tafsirul manar: 6/ 366. Tafsiru Ibn Kasir: 2/ 113-114, Bairut 1986.
Sannan akwai hadisan manzilarsa da shi kamar Haruna da Musa (a.s) ne, sannan ga hadisud Daar da ayyana shi halifa bayansa tun farkon da'awa, ga Hadisul Gadir da kowa ya yi sheda da shi ittifakan koda kuwa sun yi musun wani bangare na manufarsa ba asalinsa ba, ga su nan masu yawa da ba zasu kirgu ba.
Amma batun gado da kake cewa; Ka sani Fadima Zahara (a.s) tana daga cikin wadanda Allah ya tsarkake daga sabo sabanin masu jayayya da ita, sannan ta kafa musu hujja da Kur'ani cewa ana gadon annabawa (a.s) su kuma sun kawo hadisin aahaad wanda ba ya iya ture Kur'ani mai daraja.
Sannan jayayyar halifa na uku da matan Annabi (a.s) 'ya'yan halifa na farko da na biyu ta yanke hujja yayin da suka nemi nasu gadon bayan tsawon lokaci, yana mai yi musu raddi da cewa ai kuma kun shaida gun iyayenku da ba a gadonsa (don a hana Fadima (a.s) nata) kuka kawo wani bagidajen balaraben kauye Aus dan Hadasan wanda yake yin salla babu tsarkin bawali ya yi muku sheda kan hakan, don haka ku tashi ku ba ni wuri.
Wannan lamarin ya sanya farkon digon ba na rigimar halifa na uku tsakaninsa da Hafsa da A'isha har ya kai ga A'isah ta kafirta shi da halatta jininsa da la'antarsa!! Wannan lamurran duk suna nuna cewa Zahara (a.s) ita ce ke da gaskiya kan wannan lamarin.
Sannan kada ka manta al'amarin bai tsaya a gado ba, har ma da dukiyarta da aka kwace ta gonar Fadak, wacce magana a kanta tana da tsayi, kuma duk da Ummu Aiman da manzon Allah ya yi sheda gareta, da kuma Ali (a.s) da 'ya'yanta da makusanta sun sheda da cewa manzon Allah (s.a.w) ya ba ta, amma aka hana ta. Alhalin Jabir bn Abdullah ya gaya wa halifa na farko cewa manzon Allah ya yi mini alkawarin zai ba ni dukiya idan ta zo daga Baharain sai ya ba shi bai nemi sheda ko rantsuwa daga gareshi ba.
Don me ya sa 'yar Annabi (s.a.w) ba ta samu wannan karar ba koda kuwa saboda babanta ne: Duba kissarsa da Abubakar a cikin Majama'uz Zawa'id na Haisami: j 5, shafi: 630, H 9772.
A kalla a shar'ance idan ba a yarda da shedunta ba masu wannan daraja da tsarki to sai halifa ya rantse, idan kuwa ba haka ba, babu hujjar kwace mata wannan gona saboda ka'idar nan ta "Yadd" da ta shahara a musulunci.
Amma da kake zargin mijinta da ya kyale irin wadannan lamurra suka faru ka sani: Manzon Allah (s.a.w) ya gaya Imam Ali (a.s) cewa zai hadu da bala'o'i bayansa amma ya yi hakuri kada ya sanya takobi, kada ka manta cewa; shi ne Harunan Muhammad (s.a.w)! Sannan kuma ya yi magana kamar yadda Haruna ya yi yayin da yake cewa: "Innalkaumas tadh'afuni wa kadu yaktulunani…": Yana mai kuka a kabarin manzon Allah (s.a.w). Sannan kuma 'yar manzon Allah ba kasuwa ta tafi ba aka dake ta kamar yadda ka kawo kana mai isgili da lamarin, an balla kyauren gidanta ne aka shiga, an buge ta a ciki ta yi bari, an yi mata bulala da mari.
Abin mamaki wannan mamaya ta zo a cikin irin wadannan littattafai na AhlusSunna amma kana cewa; Sayyida Zahara (a.s) ta tafi kasuwa ne sai aka yi mata duka a can. Mu sanya ma ta tafi kasuwa ne sai aka yi mata duka a can don me za a doki 'yar manzon Allah (s.a.w) alhalin bai yi kwana uku da rasuwa ba, da wanne zata ji da rashin uba gatanta ko da duka da hauri da bulala da mari!
Ka sani Ibn Kutaiba madogara gun Sunna da mai biye masa Dabari sun ruwaito cewa: Halifa na farko Abubakar Dan Abi Kuhafa yana fada yayin da zai mutu ya yi nadama ina ma dai bai sanya an kai mamaye da samame gidan Sayyida Zahara (a.s) ba". Ina ma dai bai yi mulkin al'umma ba, ina ma dai bai …., da kin bin Usama saboda la'anar da aka yi wa wanda ya ki bi…, da kin tsayar da hakkin kisa da zina kan Khalid…" da sauransu. Duba Ibn Kutaiba Addinuri a littafin Imama Was Siyasa yana mai cewa: Abubakar ya ce: Ya yi nadamar abubuwa uku da ya sani da ya bar su bai yi ba, kuma kuma da ya bari da ya sani da ya yi su, uku kuma ina ma dai ya tambayi mazon Allah (s.a.w) game da su: sai ya ambaci ukun da ya yi nadamar yinsu kamar haka:
Na daya: Mamaye gidan zahara (a.s) koda kuwa an kulle shi a kan yakar sa ne. Na biyu: Ina ma dai bai karbi shugabanci ba ya ba wa Umar ko Abu Ubaida ya huta. Na uku: Ina ma dai ya kashe Fuja'atus Salami ko ya sake shi bai yi masa ukubar da ya yi masa da wuta da kunyatawa. Sai kuma ya kawo wanda ya so a ce bai bari ba ya yi su kamar haka; Na daya: Ina ma dai ya kashe Ash'as dan Kais. Na biyu da na Uku: Ina ma dai da ya tura Khalid bn Walid Sham ya tura Umar Iraki. Amma ukun da ya so a ce ya tambayi manzon Allah (s.a.w); Na daya: Ina ma dai ya tambaye shi waye shugaba bayansa don haka babu wani mai jayayya. Na biyu: Ina ma dai ya tambaya ko Ansar (mutanen Madina) suna da wani rabo a mulki. Na uku: Ina ma dai ya tambaya game da gadon 'yar dan'uwa da amma.
Haka nan ma Ibn Abil hadid bahanife ya kawo yana mai nakaltowa daga Mubarridu yana mai fadin wannan lamarin da muka kawo daga Ibn Kutaiba, har da karin cewa: Ina ma dai ya tambayi waye shugaba bayan Annabi (s.a.w) da kuma haddi, da cin yankan Ahlul Kitabi. Kuma ina mai dai bai mamaye gidan Fadima ba, da kin bin rundunar Usama, da barin Ash'as. da kuma fadin Ina ma dai ya yi wa Khalid bn Walid kisasi da kashe Malik bn Nuwaira, da kuma ina ma dai ya kashe Uyaina dan Hasin da Dalha dan Khuwailid.
A yanzu kana cewa ka fi Abubakar sanin abin da aka yi wa 'yar manzon Allah (s.a.w) bayan abin da ya fada, ko kana nufin a wurinka Abubakar ba adali ba ne da ba zaka sallama wa maganarsa ba!
Sannan kada ka manta lokacin da aka yi mata wannan babu laifi ga Imam Ali (a.s) domin an sanya masa igiya a wuya an ja shi kamar sa, kuma Sayyida Zahara (a.s) ta yi kuka a kofar gida kuma ta yi tawaye da sharadin janyewa idan aka sako shi!!
Ina tsawaitawa saboda na san ba ta da aibi: ina mai cewa; Imam Ali (a.s) ya san za a yi galaba kan sahabbansa da ahlin gidansa bayansa don haka ne ya yi tausasawa sabanin Imam Mahadi (a.s) wanda shi zai tsananta saboda ya san ba za a yi galaba kan mutanensa ba a bayansa.
Imam Ali ya yi kokarin dawo da mutane kan sunnar Annabi (a.s) amma ba su yarda ba, kana iya ganin misali daya daga daruruwan misalai ya yin da ya so ya hana sallar asham sai mabiyansa mayaka suka yi ca da ihu suna wayyo zai kashe sunnar Umar!!!
Kai ba ma shi ba, hatta da Manzo ya yi aiki da irin wannan domin gudun kada irin wadannan lamurra na daukar fansa su biyo baya kan alayensa al'amarin da duk da haka sai da aka yi irin wannan takurawa kansu da tarihi ya kawo!
Ka sani cewa da Imam Ali (a.s) ya dawo da Fadak to a lokacin mai ita ta rasu, sannan da ya dawo da ita ga 'ya'yanta da an sake kwacewa.
Kai manzon Allah ya dawo da mukamu Ibrahim daga inda jahiliyya suka canja masa wuri ya mayar da shi wurin da Annabi Ibrahim (a.s) ya sanya shi da umarnin Allah amma a lokacin halifa na biyu Umar dan Khaddabi sai ya dawo da shi inda jahiliyya suka ajiye shi. An yi wa Ali (a.s) magana ya sake ajiye shi wurin da Annabi (s.a.w) ya sanya shi amma ya ce yana gudun kada a dauki Ka'aba wasa. Wallahi! da ya ajiye shi inda Annabi (s.a.w) ya sanya shi da bayan wafatinsa a rannan zaka ga ya sake dawowa inda jahiliyya suka mayar da shi.
Don haka wasu abubuwan da ka ga ba su yi ba akwai hikima a ciki; me zaka ce game da manzon Allah (s.a.w) da ya ki yakar kafirai a Makka amma ya yake su a Madina duk da kuwa yana da jarumtakar da ta fi ta Imam Ali (a.s)?!.
Amma abin takaici da kake kawo batun an kashe Imam Husain kana mai nuna cewa: Ai Shi'a ne suka kashe musu malami don haka suka kashe jikokin Annabi (s.a.w). Wane malami ne mutanen da kake cewa rafilawa suka kashe wanda su kuma makiyansu suka kashe jikokin manzon Allah domin su huce haushinsu?!.
Idan kana nufin Shi'a su ne rafilawa ka ba su sunan da ba nasu ba, (koda yake wasu ruwayoyi sun nuna cewa "Saharatu Fir'aun" da suka ki lamarinsa sai ya kira su da wannan suna) Idan kuma wasu sun kashe Imam Husain (a.s) ko sun yi murnar kashe shi domin jin haushin masoyansa to wannan yana nuna batansu da tabewarsu duniya da lahira.
Ka tambayi duniya ka ji waye ya saba kashe mutane za a ba ka amsa da dai a tarihin Shi'a duniya ta san su da juriya da zaluntarsu da ake yi da su da jagororinsu Ahlul Baiti (a.s) har zuwa wannan rana tamu, abin da yake faruwa na zalunci kan Shi'a musamman a Iraki tare da cewa su ne suka fi yawa ya ishe ka misali!.
Amma batun hadisan da suka yi magana kan sahabbai da kake cewa a yi adalci a hada biyun sai in ce maka: In ganin yana da kyau ka yi wa kanka adalci, ka kawo me kake nufi, bai kamata ka kasa kawo su wa ake nufi ba, kuma ka sani addini yakan zo da dokoki ne, idan wadannan dokoki wani ya siffanta da su sai su hau kansa.
Idan ka duba da mai gani zaka samu wadannan hujjoji a fili kuma mun gabatar maka da su tun tuni, sannan kana iya karawa da wannan: Kifayatul asar: shafi: 134: inda aka yi nuni da matsayin Ali kamar Haruna da Musa (a.s) ne, da wasiyya da imamai goma sha biyu. Sharhu Ihkakul Hakk: j 13, Mar'ashi Najafi: 78: a cikin akwai magnar Fakhrur Razi da take nuna ismar Ulul amr da dogaro da wannan ayar da cewa su ma'asumai ne ba sa sabo. Sanna ka duba Zamakhshari: Manakib; 213. da Hamwini: fara'idus Simdain. Da Kanduzi a Yanabi'u: shafi: 82, Istambul. Da: sauran masdarori masu yawa matuka. Kamar Sawa'ikul Muhrika: 234. Nahajul balaga: j 2, shafi: 27. Ibn Abil Hadi: j 9, shafi: 313.
Amma game da hana mummuna ko umarni da kyakkyawa sai na ce maka; Ka sani umarni da kyakkyawa yana da sharudda idan sharudda suka fadi to ya saraya inda suka fadin. Ka duba yadda ka fada kana mai dogaro da hankali sahihi shine dole ne duk sadda kaga abin da ba daidai ba in har zaka iya kokarin gyara, to dole ne kayi. Sa'annan kana amafani da mutlakat a ko'ina ko amfani da ra'ayi wurin fassara: Ka sani "Khairu ummatin" imamai ne ma'asumai (a.s) mu kuma mu ne "nasi". Su ne wadannan da Allah madaukaki ya yi mana ni'ima da fitar da su garemu domin mu yi musu biyayya. Su ne "Ummatan wasadan" kuma mu ne "nasi" mutanen da zasu yi sheda a kanmu cewa mun bi ko mun ki umarnin Allah na biyayya garesu.
Wallahi khairu ummatin su ne (a.s)! yaya sauran mutane zasu kasance Khairu ummatin alhalin wannan al'ummar ta Annabi (s.a.w) ta kashe shi kuma ta kashe jikokinsa kuma wasiyyansa gaba daya, fiye da kisan da yahudawa suka yi wa wasiyyan Annabi Musa (a.s) mu ne (Nasara ma suka yi wa wasiyyan Isa (a.s))!
Suyudi ya ruwaito cewa: Ahlul bait (a.s) ake nufi da su a tafsirin wannan ayar. Da sauran littattafan Sunna da Shi'a masu yawa da suka nuna ma'anar da manzon Allah (s.a.w) ya bayar.
Wasu Abubuwan La'akari: Ina ganin babbar matsalarka ta farko tana cikin rashin sanin hakikanin Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w) ne. Allah madaukaki da a koyarwarku aka dauke shi da matsayin siffofi da ba su cancanci she ba, ina ganin koma wa da saninsa yana da muhimmanci gareka: wadannan siffofi da kuka ba wa Allah madaukaki da suka hada da:
Kamarsa da Annabi Adam (a.s) da tsayinsu irin daya: (fatawa bn Baz, j 4, shafi: 226). Kasancewarsa wani saurayi ne mai takalma biyu, mai gashi har baya, da korayen kafafu, yana da takalman silifa biyu na zinare, da wata ado ta zinare a fuska. (Ta'alikin Albani ga sunnar ibn Abi Asim No. 471)
Zaman Ubangiji kan al'arshi kuma yana da girma daidai al'arshin ne, sai dai al'arshin ya fi shi girma da kadan kamar girman 'yan yatsu hudu ne. (firdausil akhbar, j 1, shafi: 219). A littafin Akadul farid (j 6, shafi; 208) kuma macijiya ta kanannade al'arshin. Wannan kuwa yana nuna ta fi al'arshin tsawo sosai.
Zaman Allah kan kursiyyu: (tafsiru Dabari: j 3, s: 7)
Al'arshinsa kuwa yana kan dabbobi ne, daya mutum daya sa, daya mikiya, daya zaki. (hayatul haiwan, j 2, s: 428) da (Jahiz, kitabul haiwan, j 6, shafi: 221). Da wasu littattafai kamar al'isaba 549. tafsirud Dabari.
A wurinku duk Allah zai rube ya halaka –wal'iyazu bil-Lah! Sai kawai fuskarsa zata rage. Albani (fatawa albani: shafi: 522, 523) wani abin mamaki Albani ya yi kakkausan suka ga Buhari saboda ya yi tawilin fuska da mulkin Allah (s.w.t). a wannan ayar: "Kulli shai'in halikun illa wajhah" wanda kuwa Ubangijinsa zai halaka gaba daya sai fuska ba dai Ubangijin da ya aiko manzanni ba ne Ubangijinsa! A nan muna iya gani a fili yake cewa: "Kuna hana tawili amma kuna yin sa inda kuka ga dama, kun gwammace ku sanya Allah zai mutu ya halaka ya kare da ku yi tawili, amma saboda gyara makantar Bn Baz kun yi tawilin "Faman kana fi hazihi a'ama, fahuwa fil akhirati a'ama wa'adhallu sabila" domin ku yi kariya daga makantarsa a lahira. Don me ba ku mayar da ayoyin siffofin Allah zuwa ga muhkamata ba, amma kuka mayar da siffofin dan Adam zuwa ga muhkamata kamar "innaha la ta'amal absar…" domin ku yi kariya ga malaminku. Da ya hau kan al'arshi saboda nauyinsa sai da arshi ya yi kara. Wal'iyanzu billah!
Irin wadannan siffofin ne da kuka ba wa su Ka'abu dama da Tamin bn Aus, da Abdullahi bn Salam suka kawo koyarwar kiristanci da yahudanci cikin musulunci, sakamakon kun yi nisa da Alayen Annabi sai kuka fada cikin wadannan tarkuna nasu.
Ya zauna kan al'arshi ya dora kafa daya a kan daya yana mai jingina kan al'arshi ya kishingida sannan daga baya sai nauyinsa ya tsattsaga sammai. (tafsirud Dabari, j 25, shafi: 6).
Allah yana da 'yan yatsu hudu, ko biyar ko shida da sabanin malamanku a kai. Duba daya daga ciki a Buhari, j 5, shafi: 33. da kitabut tauhid, shafi: 225, amma shafin ya yi daidai da wanda Muhammad Salim malamin Azhar ya gyara.
Akidarku ta cewa; ana ganin Allah da idanu kamar wata: Buhari; 1, s: 195. Pop ya soki Kur'ani saboda tsarkake Allah ya goyi bayan akidar wahabiyanci ta sanya shi jiki saboda ta yi daidai da kiristanci. Duba: Littafin Al'uburu ilar Raja' a hirarsa da dan jaridar Italia. Sannan: Ubangijinku saurayi ne mai nadadden gashi dunkulalle.
Babban malam Ayatul-Lahi Kurani Allah ya tsawaita rayuwarsa yana cewa: "Kun ba wa Allah madaukaki gabobi: sau da yawa "yadullahi fauka aidihim" kuka ki tawilinta da cewa lallai dai hannu ne sosai. Amma duk da tsananin kin tawili da kuke yi idan aka zo da wani abu da ranku ba ta so sai ka ga tawili sosai: ga shi manzon Allah yana cewa: "man kuntu maulahu fa Aliyyu maulahu" "Duk wanda nake jagoransa to Aliyyu (a.s) ma jagoransa ne" a nan kam sai ga tayar da jijiyar wuya domin yin tawili iyakacin karfinku".
Sau da yawa malaman Sunna masu kyawon mahanga suka yi musun wadannan abubuwa masu yawa amma ku kuka dage kansu da kariya iyakacin karfinku. Game da Allah zan bar ka hakan, don haka sai ka yi kokarin sanin Allah, idan ka san shi to duk wadancan matsalolin zasu yi maka sauki.
Mummunan abu na biyu shi ne rashin sanin Annabi (s.a.w), wannan lamari ne mai tsananin cin rai, kun siffanta Annabi (s.a.w) da siffofin da yanzu makiya musulunci suke yi mana isgili da su kamar yadda kuka siffanta annabawa (a.s) da siffofi masu aibata su: irin wannan lamari kamar jingina wa Musa (a.s) tafiya tsirara yana bin tufafinsa, da jingina wa Sulaiman shirka da zaluncin kashe dabbobi babu wani hakki ko dalili, da kwacen mata ga Dawud (a.s) wal'iyazu bil-Lah! da sauransu. Sannan kuma kun ba wa fiyayyen halitta siffa kamar haka; Jingina masa shafar shedan sadda aka haife shi: Buhari 4, 94.
Kun jingina wa Annabi kurakurai da Umar dan Khaddabi ke yi masa gyara sai kuwa Allah ya goyi bayansa a kan abin da ya yi wa Annabi (s.a.w).
Kun dauki tawassuli da ziyarar Annabi (s.a.w) shirka. Kun dauki Annabi da rashin kimar da ibn Abdulwahab ya shelanta cewa; shi "Darish" ne, wato dan sakon da kawai ba shi da kima sai kimar sakon kawai. Kun sanya Annabi yana kokwanton annabtarsa har sai da wani kirista ya gaya masa ai kai Annabi ne sannan ya samu nutsuwa, amma wahayi ya sake jinkiri ya sake kokwanto har ya kusa kashe kansa.
Kun sanya Annabi (s.a.w) yana koyon tauhidi wurin kirista. Kun sanya Annabi yana samun galaba daga shedan da hatta da a sakonsa sai ya gafala ya yabi gumaka maimakon kushe su. Kun sanya Annabi (s.a.w) kasan darajar sauran annabawa. Kun sanya Annabi (s.a.w) yana fushi da kausasawa har ya la'ani wasu mutane ba bisa hakkinsu ba.
Kun sanya Annabi (s.a.w) bai san yadda ake auren dabino ba har shukar mutane ta lalace. Kun sanya Annabi (s.a.w) yana zalunta 'yan Badar ya kama ribatattun babu hakki kuma ya karbi fidiya babu hakki. Kun sanya Annabi (s.a.w) yana fitsari a tsaye a Bolar mutane. Kun sanya yana kuskure da yawa har sai Umar ya gyara masa.
Kun sanya shi shedan yana iya hana shi sallarsa ta dare. Kun sanya shi yana tsere da matarsa a cikin rundunar yaki a sahara. Kun sanya shi yana hana abu shi kuma ya yi. Kun sanya shi yana zuwa kallon rawar 'yan matan Afurka a masallacinsa. Kun sanya shi yana yin alwala da giyar dabino. Kun sanya shi yana samun shagaltuwa da rafkanwa a zuciya har sai ya manta ko ya yi salla ko kuwa, ya zo matansa ko kuwa! Kun sanya shi ana iya yi masa tsafi ya kama shi har ya yi wata shida bai san me yake yi ba!
Ina tambayarka don Allah ba wannan munanan tubaru da ta cikinsa kuke ganin Annabi (s.a.w) wanda har kuka sanya duniyar yamma ta fake da wadannan abubuwan tana cin mutuncinsa! Ina musulunci zai yi izza!
(Mahallin kuka) Kun sanya shi yana zo wa matansa tara a rana daya, yana zo masu suna haila, yana yin abin da bai dace ba sai ya yi bawali a tsaye, ya karbi baki yana rigingine, ya saurari waka, ya kalli rawa, ya sha Nabiz (giyar dabino)! Ya shagaltu da matarsa A'isha, ya fifita ta a kan sauran matansa, ya saurari kida da waka tare da ita, ya dora ta kan kafadarsa domin su yi kallo ta taga kumatunsa a kan nata domin kallon rawar matan Afrika, ya bar rundunarsa ta yaki ya yi tsere da ita. Kai tsarki ya tabbata ga Allah da annabinsa daga abin da suke siffantawa.
Shi ya sanya wanda yake yi wa Annabi wannan kallon zai ga bai yi wasiyya ba domin ya rena hankalin Annabi (s.a.w) ta yadda ya yi umarni da cewa; Kada mumini ya sake ya yi kwana uku bai rubuta wasiyya ba, amma kuka sanya shi ba ya yi. Koda yake kun samu maganarku ta yi karo da juna a lokacin da kuka ce ya zo ya rubuta wasiyyarsa Umar dan Khaddabi ya hana shi ya ce: ba ya cikin hankalinsa!!! Inna lil-Lahi wa'inna ilaihi raji'un!!!
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Haidar Center For Islamic Propagation
Kammala gyarawa: July 1, 2009
Ƙara sabon ra'ayi