Tattaunawa 3
Tattaunawa Ta Uku
Amma game da dawwawa: Haka ne mumini ba ya dawwama amma da sharadin ya mutu muminin, ba wanda ya take maganar Allah da Manzo (s.a.w) ya ki karba ba, alhalin ya san daga garesu take kuma ya ki imani da ita, kafircewa ayar Allah (S.W.T) karara babu wani tawili bisa sani kamar kafircewa dukkaninsa ne, kuma ayar nan ta أفتؤمنون ببعض الكتاب... tana nuni da haka ne.
Amma batun cewa Buhari bai fitar da wannan hasidin ba na sakalain; Littafin Allah da Alayen manzonsa, Na yarda da cewa bai fitar da shi ba, amma Mustadrak ya fitar da shi a matsayin abin da Buhari ya yarda da shi amma bai kawo shi a littafinsa ba. Wato hadisin bisa dokokin fitar da hadisi gun Buhari ya inganta amma ba a san dalilin da ya sa bai kawo shi ba a sahihinsa.
Sannan kuma a yanzu da zan tambaye ka mene ne abin da Manzo (s.a.w) da sahabbai suke a kai kana ganin zaka iya ganowa bayan faruwar duk abin da muka fada a baya, alhalin kowa yana ganin cewa na sa ne daidai, ingantacce!
Sannan kuma mun fadi cewa Manzo (s.a.w) ya ayyana halifofinsa masu shiryarwa. Su goma sha biyu. Wannan kuwa bayan dalilai daga littattafai, muna iya karawa da cewa; hankali ba zai iya rashin kunyar jingina rashin hikima ga mahalicci da manzonsa (s.a.w) ba, na abin da wasu suka raya cewa Manzo (s.a.w) zai ce a bi wadannan halifofi sannan sai ya ki ayyana su ya bar mutane cikin dimuwa ba su san su ba! don haka ne ma ka ga wasu suna ta kokarin hada su sun kasa!!! Suna gudun na Manzo (s.a.w) domin bangarancin Umayyanci ko mazhabanci alhalin sun kasa hada nasu.
Amma da kake ganin yaya wasu zasu so manzon rahama sanna su ki 'ya'yansa da zuriyarsa da alayensa sai in ce maka: Ka sani babu alaka tsakanin son mutum da son ‘yan’uwansa, ba dole ba ne don ka so mutum hatta da ‘ya’yansa ka so su, ka duba Manzo da Abu lahab, da Annabi Nuhu (a.s) da dansa, don haka fassara Kur’ani da ra’ayi kamar yadda na gaya maka ba abin da zai kai mu sai bata, Manzo ya fassara ma’anar zulkurba, da ma’anar Ahlul Bait, ya fassara ma’anar nisa’ana, abna’ana, amfusana, da duk wani abu da ya zo a Kur’ani. Da mai fassara zai buda lugga ne da sai ya fassara wadannan ayoyi bisa ra’ayinsa, da wannan kuwa sai ya fada cikin halaka!
Amma da kake tambayar makomar wadanda suka mutu a lokacin Annabi(SAW), ga shi kuma babu mazhabar Ahlul Baiti (a.s) alokacin tun da Annabi (SAW) na da rai, da cewar Addini ya cika kafin wafatin Annabi (SAW) koko? Ga kuma Kur'ani da hadisai na Manzon Allah(SAW)? Sai in ce maka:
Mazhabar Ahlul Bait (a.s) ana ba ta suna ne na mazhaba sakamakon abin da ya faru a duniyar musulmi, kamar yadda Manzo (s.a.w) ya ambaci jama’a zata kasu gida 73 kamar yadda ka kawo a baya, kuma kowane daga ciki yana da suna, amma daya daga cikinsu duk irin sunan da aka ba shi koda mazhaba aka kira shi, ko Shi'a’ ko rawafidawa, ko imamiyya, ko ja’afariyya, yana nan a matsayin jama’a mai tsira matukar dalili ya tabbata a kan hakan.
Don haka sanya suna baya cutarwa ko shi mazhabin ne ya ba kan shi sunan ko kuma makiyansa ne suka ba shi.
Sannan kuma addini ya cika: kuma ayar kammala shi ta sauka a ranar Gadir Khum bayan yi wa imam Ali bai’a sabanin yadda wasu suka sanya siyasa game da saukarta.
Amma kokarin da kake yi na hada alaka tsakanin fitar da Ummu Salma daga cikin Ahlul Baiti, da mas'alar haramta sadaka, hada da kokarin fassara Alayensa da aali Akilu, aali Jaafar, aali Abbas":
Sai in ce maka: A ina ka samo cewa Manzo (s.a.w) da fitar da Ummu salama yana nufin wadanda aka haramta wa sadaka ne. Muslim da Nisa’ai da Ahmad Bn Hambal da Bazzaz da Tirmizi da Tafsirai duka suna cewa Manzo (s.a.w) Ya lullube su da bargo ya ce: “Ya Ubangiji wadannan su ne Ahlin Gidana. Sannan ya fitar da matarsa, kuma ita Ummu Salama da A’isha duka sun fadi cewa ba sa ciki, Zaid bn Arkam da sauran sahabbai sun yarda ba sa ciki, kai kuma a ina ka samo cewa suna ciki.
Abin da na gaya maka ke nan na hadarin da al’umma ta fada na duba ma’anar lugga su fassara Kur’ani ba tare da duba yaya Manzo (s.a.w) ya fassara ba! Abin takaici sai ka ce al’ummar ta fi manzon Allah (s.a.w) sanin abin da aka saukar masa! Ka sani dalilin haramcin sadaka ya zo ne daban a wasu ruwayoyin, ba da wannan ne aka fitar da wannan hukunci ba. Ruwayoyi sun zo daban suna nuna haramncin sadakar ga Alayen Abdulmutallib.
Game da jimlarka ta karshe na riga na maimaita cewa Annabi ne (s.a.w) yake hujja a kanmu gaba daya, kuma bai sanya wadannan: ("aali Aliyu (dukkansu), aali Akilu, aali Jaafar, aali Abbas") cikin Ahlul Bait ba (a.s). Ya riga ya sanya mutane goma sha Uku ne a ciki da ya hada da 'yarsa da halifofinsa goma sha biyu daga alayensa na farkonsu Ali (a.s) na karshensu Mahadi (a.s). Ahlul Baiti (a.s) kalma ce da Kur’ani ya yi amfani da ita kuma ya nuna su wa yake nufi, kuma Manzo (s.a.w) ne ya fassara ya yi bayani, kuma an ce mu bi shi ne a kan hakan, sako daga Allah.
Amma abin da mai musu yake neman ji na dalilin halifancin sayyidina Ali (a.s) wadannan suna da yawa domin akwai: Hadisuddar da muka kawo a baya da manzon Allah ya yi amfani da kalmar halifana, wasiyyina, akwai hadisin manzila cewa tsakaninsa da shi kamar tsakanin Haruna ne da Musa (a.s) in ka cire annabta.
Amma batun batun cewa sayyidi Ali (a.s) ya yi maganar cewa duk wanda ya wuce su ya halaka, ya tabe. Ya kai mai musu kana iya duba hadisai kamar haka: Durrul mansur na Suyudi: j 2, shafi 60. Kanzul ummal j 1, shafi 143. usudul gaba j 3, shafi 137. Sahawi a cikin istijlabi irtika’il guraf takarda ta 24. Tabarani a mu’ujamul kabir daga Zaid dan Arkam. Ibn Hajar a cikin sawa’ikul muhrika, shafi 89. Hudubar Imam Ali (a.s) a nahajul balaga, ta 97, shafi 189.
Amma batun hadisin cewa Ahlul Baiti sune jirgin ruwan da duk wanda ya shige shi ya tsira, wanda bai haushi ba ya tabe, shi ma kana iya duba: Talkhisul Mustadrak na zahabi. Yanabi’ul mawadda na kanduzi shafi 184. sawa’ikul muhrika shafi 184. tarihil khulafa na Suyudi. Jawahirul Buhari j 1, shafi 361. alfada’il na Ahmad bn Hambal shafi 28. kai suna da dama, akwai tabarani, da kifayatut dalib na genji shafi’I, da majma’azzawa’id. Da sauransu.
Sannan batun rashin yiwuwar sabani tsakanin Ahlul Baiti basu al'amari ne da haka yake ko tantama kuma idan ka samo daya ka kawo shi mu gani, sannan kuma babu alaka tsakanin rashin sabaninsu da cewa wahayi ake yi musu kamar yadda kake kokarin alakantawa domin su ba wahayi ake yi musu ba, sai dai sanarwa ce daga Annabi (s.a.w) da suke gada kakanni zuwa uwaye zuwa 'ya'ya har zuwa na karshensu. Sannan kuma maganar da ka fada da fassarar da ka yi wa ayar nan "walaukana min inda gairil-Lahi…." tana komawa ga abin da muka ce a baya. Sannan kuma ina ganin ba mahallinta ba ne, domin Sunna ba ita ce Kur’ani ba.
Kada ka yi kuskuren da mafi yawa wadanda ba Shi'a ba suke yi na rashin fahimtar imaman Shi'a (a.s). Imam Shi'a su ne dai wadannan halifofi 12 wadanda sunnarsu ita ce hujja a kan duk wani taliki a bayan kasa. Amma sauran malaman Shi'a masu daraja kuma jagororinsu kamar sayyid Abulkasim Khu’i (Allah ya tsarkake ruhinsa) ko kuma rayayyu kamar sayyid Sistani (Allah ya tsawaita mana rayuwarsa) su mujtahidai ne da suke duba abin da ya zo daga sunnar manzon Allah da halifofinsa domin su fitar da hukuncin shari’a.
Ahlul bait (a.s) su ne Kur’ani mai magana: don haka ne ma su ne Manzo (s.a.w) ya gadarwa iliminsa tun daga Ali (a.s) birnin iliminsa shi kuma ya ba wa na bayansa har zuwa kan na karshe. Don haka duk abin da suka ruwaito yana komawa ga Annabi ne, kuma sun karfafa cewa duk abin da suka fada yana tukewa ne zuwa ga Manzo (s.a.w).
Amma tambayarka cewa don me a tarihi masu mulki ba sa son Ahlul Baiti?. Wannan lamari ne wanda yake a fili bayan sanin cewa mulki nasu ne. An tambayi Shafi’i game da Imam Ali (a.s) sai ya ce: me zan fada game da mutumin da masoyansa suka boye darajojinsa saboda takiyya (tsoro) kuma makiyansa suka boye saboda gaba, amma duka da haka (falalarsa da darajarsa) ta cika sasannin duniya biyu (gabas da yamma).
Ina ganin maganar gaba da Ahlul Bait (a.s) ta fi rana bayyana, komawa tarihi ka sha mamaki. Duba littattafan Ahlussunna kan Ahlul Bait (a.s), duba daya daga ciki kamar makatilul Talibiyyin. Sannan kuma abin da ya faru tun farko ga kakarsu wacce ta nuna zaluntarta da aka yi, ta hanyar umarni da in banda ‘ya’yanta da mijinta Imam Ali (a.s) ba wanda ya san kabarinsa.
Misalin da zan ba ka domin ka taba: Idan bayahude ya yi mana gorin cewa suna girmama jikokin Annabi Dawud (a.s) har na hawa sittin a lokacin da aka kashe jikan Manzo (s.a.w) wanda shi da kansa ya rena. To ni ina gaya maka tabbas da bayahuden ya san sirrin musulunci da abin da musulmi suka yi bayan Annabi (s.a.w) da ya yi mana gori fiye da hakan, da ya yi gorin cewa; idan mun isa mu nuna kabarin ‘yar manzonmu (a.s). Shin wannan bai isa ya sanya musulmi jin kunya ba! Shin wannan ba ya nuna zaluntar da aka yi wa Ahlul Bait (a.s) tun farkon wafatin Annabi (s.a.w)!
Sannan tambayar mai musun tafarkin Ahlul Baiti (a.s) game da sunnarsu sai na ce maka: Sunnar Ahlul Bait (a.s) ta zo ne daga manzon Allah (s.a.w) da ya ce a yi riko da ita domin ya san ba zata saba wa tasa ba, kuma ba su da wani sabani domin ita bayani ne na abin da ya bari. Ahlul Baiti (a.s) sun yi umarni ga Shi'a su yi tarayya da musulmi a komai na zamantakewar al’umma; Idan ka ga sabanin haka; kamar mu’amala maras kyau to daga Shi’a ne. Amma mas’alar azumi da shan ruwa da ka ce Shi'a suna yi daban wannan wani abu ne na fikihu da kana iya samun sabani hatta da tsakanin Sunna kansu, sannan kuma yana komawa ga fahimtar mene ne ma’anar “Lail” da aka ce “summa atimmus siyama ilal lail”.
Amma tambayarka mai cewa: A ina aka ruwaito cewa wanda yayi imani a yau ya fi sahabbai 50?. Sai na ce maka: Koma littattafan Sunna da na yi maka nuni da su: kama ga Masnad Ahmad bin Hambal har zuwa sauran, a cikin bayanin satin da ya gabata.
Amma hadisin nan na "Duk wanda ya mutu bai yi imani da imamin lokacinsa ba ya yi mutuwar jahiliyya, da kuma rashin imaninka da imamin zamaninka, da kuma nuna yawaitar jikokin Annabi (s.a.w) masu yawa haka: sai na ce maka; Ka duba littattafai kamar haka: Masnad Ahmad bn Hambal: j 2, shafi 83. 154, da j 3 shafi 446, da 4/ 96, Mustadrak alassahihain, majma’azzawa’id, kanzul ummal, Dabarani, da sauransu. Ka duba kuma; Almahim walfitan, shafi: 168, daga Imam Ali (a.s) da Mu'awiya, da ibn Umar, da Ma’azu bn Jabal da Abuzar. Don haka an karbo hadisin daga sahabbai daban-daban. Sannan kuma akwai: Yanabi’ul mawadda na Kanduzi, wani abin sha’awa shi ya fadi cewa wilayar aali Muhammad tana daga cikin jiga-jigan imani tare da cewa shi bahanife ne. sannan kuma ya karafafi maganar da wannan hadisin.
Sannan kuma da ka ce: ba ka yarda da Imamin zamani ba, to kai ne Imamin zamaninka ke nan, sai ka zama hujjar Allah a kanka, idan kuwa ka ce ba kai ba ne imamin kanka, to waye ka mika wa bai’a da jagoranci a matsayin imamin zamaninka yanzu? Domin wanda ya mutu ba shi da jagora ya yi mutuwar jahiliyya.
Sannan kuma jikokin Annabi (s.a.w) Allah ya kara mana yawansu ba su ne imamai ba wanda shari’a take ce musu: aali Muhammad ko Ahlul Bait (a.s) da ake yi wa salati. Domin na gaya maka Annabi (s.a.w) ya fassara su da cewa su sha uku ne, wadanda hudu a lokacinsa suna raye; wato; Ali da Hasan da Husain da Fadima (a.s) wadanda yake nuni da su yana fadin “Allahumma ha’ula’i Ahlu baiti” yana kuma tsayawa a bakin kofarsu kusan wata bakwai har ya yi wafati yayin sallar asuba yana maimaita wannan suna garesu. Sauran tara kuma ruwayoyi masu yawa ne suka zo da su. Amma idan kana nufin Ahlul Bait (a.s) da ma’anar lugga kamar da nufin zuriyar mutum, kamar yadda ake gaya wa sharifai a yankinmu wannan haka nan ne mana, kuma su ne wanda shari’a ta yi magana cewa bai halatta su ci sadaka ba. Wato sun yi tarayayya da aali Muhammad tsarkaka sha uku a kan wannan hukunci, sannan kuma sha biyu wato idan ka cire Zahara (a.s) su hujja ne na Allah a kan talikai kowannensu a zamaninsa. Don haka kada ka samu cakudewa.
Shari’a ba shirme take yi ba ta ce maka: wadannan miliyoyin mutane tsarkaka ne kuma ayyukansu da zantukansu da sauransu hujja ne. Don haka yana da kyau ka san me Shi'anci yake cewa: kuma ka riga ka sani cewa; hatta da mafiyawan shi'a a yankunanmu ba zurfi suka yi cikin sanin mazhabin Ahlul Bait (a.s) ba.
Amma maganarka ta ce; Don Allah a koma ma Kur'ani da ingattatun sunnonin Annabi (SAW) ko a samu tsira duniya da lahira. Wannan shi ne abin da ya kamata ga dukkan musulmi, amma ka sani cewa: ba zaka iya sanin Kur’ani ba ko sunnar Annabi sai da abin da shi annabin ya yi bayani. Kuma maganganunka suna nuna cewa: har yanzu ba ka kawo ayar Kur’ani daya ba da ka fassara ta daidai kamar yadda Annabi ya fassara, ka ga ke nan akwai bukatar ka samu nutsuwa sosai da tunani kan cewa yaya Annabi ya fassara Kur’ani sabanin ra’ayoyin sauran mutane.
Kuma su waye ya bari masu bayanin abin da ya bari na sunnarsa da zasu kasance makoma idan al’umma ta yi sabani. Bai kamata ba domin wani yana balarabe ko ya san larabci sai ya hau Kur’ani da fassara yadda ya so, idan haka ne sai mu ce: muna sha’awarku larabawa kun san Kur’ani, alhalin ba haka ba ne. Manzo (s.a.w) ya yi bayanin ma’anar Ahlul Bait, da zulkurba, da salla, da zakka, da humusi, da alwala, da aure, da azumi…, da dukkanin wani hukunci, amma kiyasi da ra’ayi bisa rashin sani ko son rai sun sanya jirkita da karkatar da ma’anar kalmomin addini, da hukuncin shari’a.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Haidar Center For Islamic Propagation
Kammala gyarawa: July 1, 2009
Ƙara sabon ra'ayi