Dalilan Matsin Lamba Kan Kasar Iran
Dalilan Matsin Lamba Kan Kasar Iran
Jagora Ya Fayyace Dalilan Makiya Na Matsin Lamba Kan Kasar Iran.
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewar gagarumin ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke samu ne a fuskokin daban daban na ilimi ke kara fusata makiya.
A ganawar da ya yi da 'yan Majalisar Kwararru masu zaben jagoran Musulunci a kasar Iran a yau Alhamis: Jagoran juyi juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Uzma Sayyid Ali Khamene'i ya bayyana irin gagarumar rawar da al'ummar Iran ke takawa a fagen kara bunkasa ci gaban kasarsu, tare da jaddada cewar babban abin da ke kara fusata makiya shi ne ganin yadda al'ummar Iran ke kara samun ci gaba a fannonin ilimummuka daban daban.
Jagoran ya kuma jaddada cewar matsin lamba da kakaba takunkumi da kasashen yammacin Turai ke yi kan kasar Iran kokari ne na neman ganin al'ummar Iran sun mika kai ga munanan manufofinsu. Kamar yadda jagoran ya jaddada cewar takunkumin da makiya ke kakabawa Iran ya kara zaburar da kwararrun kasar musamman matasa kara matsa kaimi a fagen ilimi da bunkasa fasahar makammashin nukiliya na zaman lafiya, don haka takunkumin sai ya zame alheri ga kasar Iran.
Ƙara sabon ra'ayi