Yamutsin Kasar Masar

Yamutsin Kasar Masar
Jami'an Tsaro Masu Gadin Fadar Shugaban Kasar Masar sun Bar Wuraren aikinsu
Jami'an tsaron kasar Masar masu gadin gidan shugaban kasar Mohammad Mursi sun bar wurareren aikisu sun kuma hadewa sauran abokan aikinsu wadanda suka fara zaman dirshe a kusa da babban cibiyar yan sandan kasar da ke birnin Alkahira. Kamafanin dillancin labaran AFP na kasar faransa ya nakalto wasu kafafen yada labarai cikin kasar Masar suna cewa jami'an tsaro masu tsare fadar shugaban kasa sun hadewa tokwarorinsu wadanda suka fara zaman dirce a kusa da babban ofishin yansanda na birnin Alkahira tun jiya Alhamis 7 ga watan maris inda suke bukatar ministan harkokin cikin gidan kasar ya yi murabus daga mukaminsa. Jami'an tsaron har'la yau suna zargin ministan cikin gida da amfani da su don cimma manufofinsa na siyasa. Bugu da kari jami'an tsaron sun bukaci ma'aikatar cikin gidan kasar Masar ta fayyace iyakan ayyukan da ake bukatan jami'an tsaro suyi  a aikin da suke yi da kuma samar masu kayakin aiki da makamai wadanda zasu kare kansu da su a lokacin da suke fuskantar masu zanga zanga da suke kan titunan biranen kasar ba dare ba rana a cikin yan kwanakin nan. 

Ƙara sabon ra'ayi