Takunkuma Kan Kasar Iran
Takunkuman Da Kasashen Yamma Suka Dorawa Kasar Iran Ta Rashin Hakali Ne
Limamain da ya jagoranci sallar jumma'a a nan Tehran Aya. Mohammad Ali Muvahhidi Kirmani ya bayyana takunkuman da kasashen yamma suka dorawa kasar iran a matsayin rashin tunani Limamin ya kara da cewa a bayyane wadan nan kasashe suna nuna cewa sun dorawa kasar Iran takunkuman ne don shirinta na makamacin Nuclear amma manufarsu ta gaskiya ita ce fada da tsarin musulunci wanda yake jagorancin kasar Iran fiye da shekaru 30 da suka gabata. Aya. Kirmani ya ce tururuwan da mutanen kasar Iran suka yi, suka fito don halattar jerin gwanon cika shekaru 34 da nasarar juyin musulunci a kasar Iran ya nuna cewa suna goyon bayan tsarin musuluncin da ke jagorancin kasar. Da ya juya bangaren matsalolin tattalin arziki wanda mutanen kasar suke fama da su kuma, Aya. Kirmani ya bayyana cewa wasunsu, sanadiyar takunkuman da aka dorawa kasar ne, a yayinda wasu kuma daga cikin gida ne. Limamin ya ce hadin kai tsakain jami'an gwamnati da kuma mutanen kasar zai taimaka wajen warware mafi yawan wadan nan matsaloli. A wani bangare na khudubarsa kuma, Aya. Kirmani ya yi nuni da ganawar jagoran juyin juyan halin musulunci da majalisar kwararru masu zaben jagora, inda jagoran ya jadda muhimmancin fitowar mutane zuwa kada kuri'arsu a zabubbuka masu zuwa a shekara mai kamwa.
Ƙara sabon ra'ayi