Rayuwar Duniya

Rayuwar Duniya
Rayuwar duniya ita ce farkon rayuwar da dan Adam yake fuskanta domin gina ta lahira, don haka ne zamu ga imam Ali (a.s) ya muhimmantar da ita matuka a cikin kalamansa masu daraja. Imam Ali (a.s) ya fada yayin da ya ji wani mutum yana sukan duniya: "Ya kai mai zagin duniya, mai ruduwa da rudinta, mai yaudaruwa da barnarta, yaya kake ruduwa da duniya sannan sai ka zarge ta, kai ne mai laifi gareta ko kuwa ita ta yi maka laifi, yaushe ne ta kawar da hankalinka ko ta yaudare ka? Shin don ta kayar da iyayenka saboda tsufa, ko kuma saboda makwancin uwayenka karkashin kasa? Mutum nawa ka yi jinya da hannunka, ko ka sanya kuma nawa ka yi wa hidima suna rashin lafiya da kake nema musu waraka, kana mai siffanta musu magani -yadda za a yi amfani da shi- tausayawarka ba ta amfani daya daga cikinsu ba, kuma ba su abin bukatarsu bai magance musu komai ba, kuma ba ka iya kare shi ba da karfinka, duniya ta nuna maka ita wace ce, kuma faduwarsa ita ma faduwarka ce. Hakika duniya gidan gaskiya ce ga wanda ya gaskata ta, kuma gidan lafiya ce ga wanda ya fahimce ta, kuma gidan wadata ce ga wanda ya yi guzurinta, kuma gidan wa'azi ce ga wanda ya wa'aztu da ita, masallacin masoya Allah ce, masallatar mala'ikun Allah ce, kuma masaukar wahayin Allah ce, wurin kasuwar waliyyan Allah ne, ku nemi rahama a cikinta, ku ribaci aljanna a cikinta. Waye wannan da yake zaginta alhalin ta san 'ya'yanta, kuma ta yi kira da rabuwa da ita, ta yi jimamin rashinta da rashin ma'abotanta.
Sai ta misalta musu bala'i da bala'inta, ta kwadaitar da su zuwa ga farin ciki da farin cikinta, sai ta huta da lafiya, ta wayi gari da musiba, tana mai kwadaitarwa da tsoratarwa, tana mai firgitarwa da yin gargadi. Sai wasu mazaje masu wayewar gari da nadama suka zage ta, wasu kuwa suka yabe ta ranar kiyama, duniya ta tunatar da su sai suka tunatu, ta yi musu magana sai suka gaskata, ta yi musu wa'azi sai suka wa'aztu". Nahajul-balaga: Hikima: 126.
Idam muka duba wannan bayani mai kima a cikin wannan hikimar zamu gat a tattaro bayanai masu kima kamar haka; fadinsa ga wannan mutumin "Ya kai mai zagin duniya, mai ruduwa da rudinta, mai yaudaruwa da barnarta, yaya kake ruduwa da duniya sannan sai ka zarge ta” wannan yana nuna mana cewa duniya ni’ima ce daga ni’imomin Uabangiji, kuma mai zaginta mai butulci ga wannan ni’ima yana kan kuskure, sannan ita wannan duniya tana nan duniya ga mai aiki na gari, da mai aiki na laifi babu bambanci, kai ba ta da bambanci tsakanin annabi daga annabawa da kuma wani kafiri daga kafirai, su mutane su ne suke lalacewa sai su jingina abin ga duniya. Da lalacewa daga duniya take da ba a samu wani mutum na kirki ba, a nan ne zamu ga imam Khomain shugaban juyin musulunci a Iran yana cewa: Duniya wurin Allah ne, kada ka yi sabo a wurin Allah.
Sai fadin imam Ali (a.s) cewa: “kai ne mai laifi gareta ko kuwa ita ta yi maka laifi, yaushe ne ta kawar da hankalinka ko ta yaudare ka? Shin don ta kayar da iyayenka saboda tsufa, ko kuma saboda makwancin uwayenka karkashin kasa? Mutum nawa ka yi jinya da hannunka, ko ka sanya kuma nawa ka yi wa hidima suna rashin lafiya da kake nema musu waraka, kana mai siffanta musu magani -yadda za a yi amfani da shi- tausayawarka ba ta amfani daya daga cikinsu ba, kuma ba su abin bukatarsu bai magance musu komai ba, kuma ba ka iya kare shi ba da karfinka, duniya ta nuna maka ita wace ce, kuma faduwarsa ita ma faduwarka ce”.
A nan ma muna iya ganin karfafar waccan maganar a fili domin idan muka duba zamu ga babu wani laifi da duniya ta yi wa mai zaginta, ko mai zarginta, domin idan mutuwa ce da iyayensa suka yi laifinta to kowa ma babansa ya mutu, kuma tsufa da mutuwa duk halitta ce ta mutum da dole su riske shi, kuma duk wani wanda ya yi zagin a kansu to yana koma wa kansa ne, domin ya yi jiyyar mutane da yawa da ba ya iya kare su daga mutuwa ko rashin lafiya, wadannan lamurra ne da suke hannun ubangiji madaukaki mahaliccin duka ba ki daya.
Sannan imam Ali (a.s) ya ce: “Hakika duniya gidan gaskiya ce ga wanda ya gaskata ta, kuma gidan lafiya ce ga wanda ya fahimce ta, kuma gidan wadata ce ga wanda ya yi guzurinta, kuma gidan wa'azi ce ga wanda ya wa'aztu da ita, masallacin masoya Allah ce, masallatar mala'ikun Allah ce, kuma masaukar wahayin Allah ce, wurin kasuwar waliyyan Allah ne, ku nemi rahama a cikinta, ku ribaci aljanna a cikinta. Waye wannan da yake zaginta alhalin ta san 'ya'yanta, kuma ta yi kira da rabuwa da ita, ta yi jimamin rashinta da rashin ma'abotanta”.
A nan ma muna da abin lura cikin wadannan kalamai masu daraja yayin da yake nuni zuwa ga cewa wannan duniyar kamar yadda take mashaya ce gun fasikan bayi, wadanda suka dauka cewa babu mahalicci, suke yin aikin da suka ga dama na masha’a da alfahasha, to su sani cewa ita gidan Allah ce kuma dakinsa, wannan yana nuna mana cewa ashe ba komai ba ce duniya sai gidan bautar Allah madaukaki, wannan kuwa yana gaskata fadin Allah madaukaki cewa; “Ban halicci mutum da aljan ba sai don su bauta mini”. Don haka a fili yake cewa wannan magana ta Imami mai daraja da girma tana fassara wannan ayar a fili cewa duniya masallaci ce.  Kuma mun san masallaci wuri ne mai tsarki, kuma duk wuri mai tsarki ana girmama shi, a tsarkake shi, a darajanta shi ne.
Kamar dai fada ce ta wani sarki mai adalci da ake girmama shi saboda kasancewarsa abin so a zukatan raunanan mutane, to ina ga wanda yake shi ne mai bayar da duk wani abu da muka mallaka, da mu da abin da muke mallaka duk nasa ne, babu wani abu da ba na sa ba. Samuwarmu da lafiyarmu, da iskar da muke amfana da ita, da ruwan sha da muke amfana daga gareshi, da ni’imomin ji da gani, da shaka, da shafa, da dandano duk daga gareshi suke. Da duk duniya sun taru a kan su yi mana digo daya na ruwa, ko shaka daya ta iska da ba su iya ba, don haka wannan duniya mahalartar wurin Allah ce, don haka a mahalartar wurin Allah kada mu saba masa.
Imam Ali (a.s) ya ci gaba da cewa: “Sai ta misalta musu bala'i da bala'inta, ta kwadaitar da su zuwa ga farin ciki da farin cikinta, sai ta huta da lafiya, ta wayi gari da musiba, tana mai kwadaitarwa da tsoratarwa, tana mai firgitarwa da yin gargadi”.
A nan Imam Ali (a.s) yana nuna mana cewa duniya gidan surki ce, mu sani duniyoyi sun kasu gida uku: Duniyar da muke ciki wacce muke samuwa cikinta bayan cikin uwa, sai kuma duniyar barzahu da ake cirata zuwa gareta bayan mutuwa, sai kuma duniyar lahira, wacce ake cirata zuwa gareta bayan busa, sai mutane su tashi daga barzahu zuwa lahira.
Ita wannan duniyar tana cakude da kyawu da muni duka, sai dai wadanann abubuwan biyu suna zuwa ne daga zabin da mutane suka yi ne. Sai wani ya yabe ta saboda ya zabi hanya ta gari, wani kuwa ya soke ta saboda ya zabi mummunar hanya, wani ya yabe ta saboda jahilci, wanda kuwa yake da ilimi ya san kansa, ya san mahaliccinsa, ya san me yake yi sai ya yabe ta, saboda ya san cewa mahalatar wurin Allah ce, sai ya nemi makoma mai kyau tun daga wannan daki na Allah (s.w.t), sai ya yi nisa da abin da zai kai shi ga tabewa a cikin duniya da makomarsa.
Sai duniya ta bayar da lafiya da farin ciki da yalwa da ni’ima ga wanda ya san kansa, ta bayar da bala’i, da bakin ciki, da kunci ga wanda ya jahilci kansa da ubangijinsa. Domin ita wannan duniyar ita ce aljanna da wuta, domin tun daga nan ne aka tanadarsu, kuma tun da mutum yana da zabi a kansa, shi ne yake zabar shiga wuta ko aljanna, kamar yadda shi ne yake zabar ni’imar duniya ko bala’inta.
Kowane mutum yana da nasa aiki, kuma kowane mutum yana da inda ya fuskanta, don haka kowane mutum yana da nasa sakamako gwargwadon abin da ya zaba ya aikata. Wannan duniya babu ruwan Allah game da ni’imarta, yana bayar da ni’imarta ga duk wanda ya zabi hanyar samun ni’imar, kamar yadda yake bayar da lahira ga dukkan wanda ya zabi ni’imarta tun a nan duniya.
Amma fadin Imam Ali (a.s) “Sai wasu mazaje masu wayewar gari da nadama suka zage ta, wasu kuwa suka yabe ta ranar kiyama, duniya ta tunatar da su sai suka tunatu, ta yi musu magana sai suka gaskata, ta yi musu wa'azi sai suka wa'aztu".
Imam yana nuna yadda mutum yake da butulci, shi ne zai zabi abin da yake kansa, amma sai ya zargi wani abu daban. Mutum ne ya ki karbar sakon Allah a duniya, shi ne ya ki addinin Allah, shi ya ki wasiyyan da annabawan Allah suka bari, al’ummu duka abu guda suka yi game da sakon Allah.
Kamar yadda yahudawa suka ki wasiyyan annabi Musa (a.s), kuma kiristoci suka ki wasiyyan annabi Isa (a.s), haka nan wannan al’ummar ta annabi Muhammad (s.a.w) ta ki wasiyyansa. Sai suka riki littattafan suka watsar da wasiyyan, don haka ne littattafan ba su hana su rarraba da fadawa cikin bala’i ba, domin sun ki mai fassara littafi, sai suka bi ra’ayoyinsu, sai suka fada cikin faganniya, sannan duk a nan sai su zargi wasunsu na daga zamani, da duniya, da sauransu, sai suka ci gaba da dimuwa maras iyaka, sannan da bala’i a lahira.
Sannan haka nan a cikin littafin a Hikima ta  181, Imam Ali (a.s) yana cewa: "Hakika mutum a wannan duniya allon hari ne da lokutan mutuwa suke harinsa su kafe cikinsa, abin hari ne da musibu suke gaggauta masa, a tare da kowace hadiyar ruwa akwai shaka, akwai kuma makalewa tare da kowace loma. Kuma bawa ba ya samun wata ni'ima sai ya bar wata, kuma ba ya fuskantar wata rana ta rayuwarsa sai ya rabu da wata zuwa ajalinsa. Mu 'yan'uwan mutuwa ne, kuma rayuka masu kafuwa cikin halaka ne, yaya kuwa -idan haka ne- zamu nemi wanzuwa alhalin ga dare da rana nan ba su taba daga wani abu sama ba sai sun gaggauta komowa don rusa abin da muga gina shi, da rarraba abin da muha hada shi".
A nan yana nuna mana hakikanin mutum a wannan duniya cewa shi waye, mutum ba komai ba ne sai rayayye mai mutuwa, kuma wannan mutuwar zatinsa ce, don haka ne duk wanda yake tsoron mutuwa yana tsoron kansa ne. A nan zamu ga cewa Imam Ali (a.s) ya riga ya yi bayanin mutum da cewa shi mai rai ne mai mutuwa tun kafin a haifi irin su “Nietzsche, Friedrich Wilhelm1844-1900” da sama da shekaru dubu da dari biyu.
Duba yadda Imam Ali (a.s) yake cewa: "Hakika mutum a wannan duniya allon hari ne da lokutan mutuwa suke harinsa su kafe cikinsa”. A nan zamu ga mutum an yi bayaninsa a matsayin mai rayuwa ne mai mutuwa kowane lokaci, ta yadda a koda yaushe mutum yana iya mutuwa, don haka ne ma zamu ga Imam Sadik (a.s) yana fadin cewa mutum yana da ajali biyu ne, na farko ajalun musamma wanda yake ajali ne da ba yadda zai ketare shi, da kuma wani ajali da ake kira ajalun mu’allak, shi kuma ajali ne da koda yaushe yana iya samun mutum. (Tashihu i’itikadatul imamiyya: Sheikh Mufid; s 66), kuma shi ne Allah ya yi nuni da shi cewa: “Ba a raya wani abin rayawa, kuma ba a ragewa daga rayuwarsa sai yana cikin littafi. Surar Fadir: 11. kamar yadda wasu hadisai masu yawa suka zo da nuni kan rage shekaru saboda wasu sabo, ko kara su saboda wasu ayyukan alheri, kamar sadar da zumunci, ko sadaka.
Idan mun duba zamu ga ajalun musamma idan ya zo ba a iya ketare shi, amma ajalun mu’allak ana iya ketare shi, kamar wanda za a rubuta yau zai mutu da hadari, sai kuma ya yi sadaka da safe, sai Allah ya shafe masa wannan kamar yadda ya zo a kissar annabi Isa (a.s) da ya bayar da labarin wata amarya da zata mutu amma sai ta yi sadaka, wacce a saboda haka ne aka kare ta daga saran maciji da aka ga gawarsa a karkashin abin kwananta da ita da angonta.
Sannan idan mun duba fadin Imam Ali (a.s) cewa: “abin hari ne da musibu suke gaggauta masa, a tare da kowace hadiyar ruwa akwai shaka, akwai kuma makalewa tare da kowace loma”.  Wannan siffofi na mutum yana nuna mana cewa mutum an hada shi daga abubuwa biyu masu karo da juna, da aka cakuda masa su, sai aka cakuda masa ni’ima da bala’i, kamar dai yadda duniya ta kafu ne kan nagetib da fozitib masu dauke da alamar korewa da tabbatarwa, wadanda idan babu daya ba yadda za a samu rayuwa.
Haka nan ne aka dora rayuwar mutane da samuawrsu, sai aka surka musu wadannan halittu biyu domin rayuwa ta yiwu, idan ba haka ba, da ba a samu rayuwa ba. A takaice muna cewa wannan duniyar gidan surki ce tsakanin abubuwa biyu da muna iya cewa idan babu dayansu to babu rayuwa. Kamar yadda aka samar da mace da namiji, da zafi da sanya, da lafiya da rashinta, da jahilci da ilimi, da danshi da bushewa, da sauran halittu masu kishiyantar juna domin rayuwa ta yiwu a wanan duniyar.
Sannan fadinsa (a.s) cew: “Kuma bawa ba ya samun wata ni'ima sai ya bar wata, kuma ba ya fuskantar wata rana ta rayuwarsa sai ya rabu da wata zuwa ajalinsa”. Yana nuni ga abin da muka kawo yanzu.
Amma fadinsa cewa: “Mu 'yan'uwan mutuwa ne, kuma rayuka masu kafuwa cikin halaka ne, yaya kuwa -idan haka ne- zamu nemi wanzuwa alhalin ga dare da rana nan ba su taba daga wani abu sama ba sai sun gaggauta komowa don rusa abin da muga gina shi, da rarraba abin da muha hada shi". Wannan yana nuni da cewa duniya ba wurin wanzuwa ba ne.
Sannan a cikin wannan maganar akwai nuni da cewa ba mu da ikon mu yi yadda muka so sai yadda wani karfi da yake sama da mu ya so, da wannan muna iya fahimtar cewa akwai mahalicci mai karfi da ya fi kowa, wanda yake bata abin da muka tsara, yake tsara abin da ba mu shirya masa ba.
Kuma duk wani mai rayuwa a wannan duniya abin rinjaya ne gun wanann karfi, wannan karfin shi ne Allah mahalicci, mai iko da irada, wanda ya halicci mutuwa da rayuwa.
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com  
Haidar Center for Islamic Propagation
Monday, May 17, 2010

Ƙara sabon ra'ayi