Kimar Mutum
Kimar Mutum
Kimar Mutum
Written by Hafiz M Sa'id
Sunday, 30 May 2010 11:09
Mutum halitta ce mai girma daga cikin halittun Allah madaukaki wanda ya girmama shi fiye da kowace halitta, sai dai wannan halitta mai girma da kima mai wuyar sha’ani yana iya kaiwa matakin da ya fi kowace halitta kamar mala’iku madaukaka, kamar yadda yana iya kaiwa mafi munin halitta da yake kasan darajar alade, kuma wannan lamari ya sanya mutum mai wuyar sha’ani, murdadde.
Daya daga cikin mafi girman ni’imar da Allah ya yi wa mutum ita ce bude masa hanyoyi biyu na kamala da na kaskanta. Madaukaki yana cewa: “Mu mun nuna masa tafarki ko ya kasance mai yawan godewa ko mai yawan kafircewa”. (Insan: 3).
Da fadinsa: “Mun shiryar da shi tafarki biyu” (Balad: 10).
Domin mutum ya samu daukaka da kamalar dan’adamtaka yana bukatar ya samar da alaka uku ne wacce kowacce daga cikin tana da dokoki da hanyoyi da zai iya kyautatawa. Wadannan alakokin mafi muhimmanci da kima da daraja da girma ita ce alaka da mahalicci, sannan sai alaka da mutum, sai kuma alaka da sauran halittu.
Sannan wadannan alakokin suna shiga cikin juna ne, ba su kasance hannun riga da junansu ba, don haka kyautata kowacce daga cikinsu tana da alaka da kyautata sauran. Idan mutum ya kyautata alakarsa da Allah madaukaki to yana nufin ya kyautata duka ukun ne. Sannan a wannan rubutun namu zamu karfafi bayani kan alakar mutum da dan’uwansa mutum ne.
Idan mun duba alakar mutum da dan’uwansa mutum zamu ga mutane sun kasu gida biyu; imma dai suna da kimanta jinsinsu na mutane ko suna kaskantar da su.
A ilmance an sanya wannan lamarin a matsayin ma’aunin gane mutum mai kima da daraja, domin idan mutum mai kima ne sai ya kimanta dan Adam domin kansa yake nunawa ta yadda kimarsa takan sanya shi jin sauran mutane suna da kima, amma idan kaskantacce ne sai ya yi tsammanin kowa ma haka yake.
Kuma haka lamarin yakan juya ga wanda aka girmama idan mai kima da daraja ne sai ya girmama ka, amma idan mai kaskanci ne sai ya yi takama. Masu hikima suna cewa: “Idan ka girmama mai daraja sai ka mallake shi, idan kuwa ka girmama kaskantacce sai ya yi dagawa da girman kai” (Al’mu’utamaratus Salas: Husain Shakiri/ s 147).
Kamalar Annabi (s.a.w) da imamai magadansa masu daraja ce ta sanya mu gane cewa su ne masu mafi daukakar darajoji a cikin kowane fage na ilimi da sani, da kyautata alaka da mahaliccinsu da sauran bayi mutane, da kuma sauran halittu, fiye da kowane mahaluki.
Duba abin da ya zo a littafin Risalatul Hukuk na Imam Zainul’abidin (a.s) (s; 7) yayin da wata baiwarsa take zuba masa ruwa yana yin alwala da buta, sai butar ta subuce ta fada fuskarsa ta ji masa ciwo, sai ya daga fuskarsa ya kalle ta. Sai ta ce masa: Allah madaukaki yana cewa: “Da masu hadiye fushi”, sai ya ce: Na hadiye fushina. Sai ta ce: “Da masu yin afuwa”. Sai ya ce: “Allah ya yi miki afuwa”. Sai ta ce: “Allah yana son masu kyautatawa”. Sai ya ce: Ke ‘ya ce saboda Allah! (ya ‘yanta ta).
Duba yadda wannan baiwa tasa ta rotse masa fuska amma sakamakon fasa wannan fuska mai daraja shi ne ma’abocin wannan fuska madaukakiya ya ‘yanta wannan baiwa. Ina ne mutum zai iya samun irin wannan mu’amala, da wannan dabi’a mai tsananin yalwa da girmama in ba a irin wadannan cikakkun mutane masu daraja ba!.
Kamar yadda Ali bn Yusuf al-Hilli ya kawo a cikin littafin nan “Al’adadul Kawiyya/ s 155” game da wata ruwaya ta Sufyanus Sauri cewa ya shiga wurin Imam Sadik (a.s) sai ya gan shi duk launinsa ya canja, sai ya tambaye shi game da hakan, sai ya ce: “Na kasance na hana mutanen gidana hawa saman daki ne, na shiga gida sai ga wata baiwata wacce take renon wasu yarana ta hau saman tsani ga yaro tare da ita, da ta gan ni, sai ta tsorata ta dimauce, sai yaron ya fado kasa ya mutu. Sam launina bai canja ba saboda mutuwar yaron, sai dai launina ya canja ne saboda firgicin da ta samu saboda ta gan ni, sannan sai ya ce mata: Ke ‘ya ce saboda Allah, babu komai kan ki -ya fada mata haka har sau biyu-.
Idan ka duba wadannan masu daraja da yadda suka san ubangijinsu sai wannan ya sanya su sanin dan Adam da sauran halittu, sai suka kasance babu wani abu na cutarwa da yake iya faruwa daga garesu zuwa ga wani halitta, maimakon haka sai dai ma su samu cutuwa kuma su yafe.
Don haka sai suka kasance rahama ga dukkan talikai, fitilar haskakawa domin gane gaskiya daga bata, tudun tsira. Kuma manzon rahama (s.a.w) ya siffanta su da cewa su ne tudun tsira yayin da yake kamanta su da jirgin Annabi Nuhu (a.s), da kofar tubar Banu Isra’il.
A yanzu ne zamu gane cewa; domin kowane mutum ya kasance rahama ga talikai dole ne ya kasance ya san ubangijinsa, ya kiyaye kansa, da wannan ne zai kasance haske mai haskakawa duniya, fitilar da take kona kanta domin wasu su samu haske.
Yanzu zaka kwatanta wadannan masana Allah (s.w.t) da kaskantattun bayinsa wadanda ba su san komai ba sai kawukansu, ba su san Allah ba. Sannan ga cututtukan rayi sun cika su, idan kana neman mai girman kai da jiji-dakai ka same su, to ka kai magaryar tukewa. Su suna dagawa saboda kawai sun ga sun isa “Lallai mutum yana dagawa, saboda kawai yana ganin kansa ya wadatu”(Alaki: ).
Wasu mutanen babu wanda ya tsira daga sharrinsu, sannan na kasa da su yana gigicewa saboda halayensu, sannan mafi yawan al’amuran al’umma suna hannun irinsu a cikin kasashe. Akwai misalin wani ambasadan Nijeriya a wata kasa (a 2003-2007) wanda kamar yadda bai san kimar kasarsa da al’ummarsa ba. Rashin mutuncinsa ya mamaye hatta da gidansa ta yadda matarsa ta yi mummunan abin da zai ba ka mamaki ta kori mai yi mata hidimar shara da wanke-wanke domin kawai ta fasa mata tangaran, alhalin santsinsa ne ya sanya kubucewarsa daga hannunta.
Duba nisan da yake tsakanin irin wadannan mutane biyu, tsakanin kamilin mutum masanin Allah cikakken sani wanda yake jin zafin tsoratar da baiwarsa ta yi alhalin ta kashe masa da, amma ba wannan ne tunanin da yake damusa ba, sai tunanin tsoron da ya same ta sakamakon laifin da ta yi, kuma wannan ya sanya shi ‘yanta ta. Da kuma mutumin da ya dulmiye cikin kogin son duniya da tsananin jahiltar Allah madaukaki, da kallon bayi a matsayin abin biyan bukatarsa kawai ta yadda wannan kungurmin jahilin mutum wanda ya narke kan son duniya da ganin girmanta, da jahiltar Ubangijinsa da kuma rashin sanin kansa, ya dauki tangaran dinsa ya fi dan Adam kima, ta yadda duk wani wulakanci yana iya yi masa saboda tangaran dinsa!.
Wani abin da ya fi wannan rashin imani shi ne na wani mutum maras mutunci da ya taba kade wani yaro ya mutu sai iyayen yaron suka yafe, shi wannan mutumin ba ma dan Nijeriya ba ne. Amma da yake mutumin ba shi da kimar mutuntaka da dan adamtaka tare da shi ko kwarzane, sai ya rika yi musu dariya bayan ya tafi da shi da abokansa ‘yan kasarsa, yana mai cewa; ya dauka zai biya diyya ne, ashe wadannan mutanen wawaye ne, yanzu sun bar masa diyyar kyauta kenan!.
Wannan mutumin ya cika maras kima, kuma ya kai matukar makurar kaskanci, yayin da ya dauki alherin da wasu suka yi masa abin da yi wa dariya da isgili!. Lallai maganar masu hikima ta gaskata yayin da suke cewa: Idan ka girmama mai karimci sai ka mallake shi, amma idan ka girmama kaskantacce sai ya yi dagawa. Domin babu wani mai fahimtar alheri sai ma’abocin alheri, amma kaskantaccen mutum wanda bai san alheri ba, idan ka yi masa alheri sai ya yi dagawa, ko ya ga wani wayo ne ya ba shi hakan. Misalin Karuna babbban misali ne a wannan fage yayin da yake cewa: “Ai duk sanina (dubarata) ne suka ba ni wannan dukiya...” (Kasas: 78).
Idan mutum ya daukaka yana da matukar girma da daraja, amma idan ya fita daga kimar nau’insa, sai ya koma mafi kaskantar halittun duniya. A ilimin Mantik ana yin bayanin cewa; mutum shi ne mai rai mai hankali, sai ga mutum a yau ya komai mai rai mai farautar dan’uwansa mutum. Ba zaka ji komai ba a duniya sai kisa, da fashi, da yaudara, da zambo, da gaba, da kiyayya, da fushi, da rashin zaman lafiya, da rashin tsaro, da talauci, da cututtuka, da makamantansu. A Jiya ne ma wani yake bugo mini waya cewa; Ai ‘yan fashi sun tare hanyar su Tsohon Gwamna Abubakar Rimi, sai ya samu bugawar zuciya sai ya mutu kafin a karasa asibiti!.
Kuma haka nan kissar take ga dubunnai da miliyoyin mutanen da suke rayuwa a duniya, a kullum firgici, da tsoro sai sun yi kisa bisa dalilai iri-iri. Kamar yadda a kullum Allah ne kawai ya san yawan matan da ake zubarwa mutucinsu ta hanyoyi mabambanta mafi muninsu shi ne fade!.
Wannan kuwa ita ce makomar dan Adam matukar ya yi nisa da sakon Allah, a koda yaushe dan Adam ya yi nisa daga tafarkin haske, to zai zurfafa cikin duhun faganniya kenan.
Don me ya sanya mutum ba zai yi tunanin meye matsalar ba! Don me ba zai koma cikin hankalinsa ya yi tunani ba?! Shin muna tsammanin haka Allah madaukaki yake son duniya ta kasance ne?! Shin muna tsammanin cewa Allah bai yi duniya don rahama ba, ya yi ta ne don wahala?! Shin muna tunanin cewa wadannan abubuwan da suke faruwa ba su da dalili ne?! kuma shin mun sanya tunani domin ganin mun kama hanyar warwara?!
Ganin halin da duniya take ciki ya sanya mutanenta sun yanke kauna daga samun gyara, wannan kuwa shi ne ya fi komai muni, domin ba masu yanke kauna sai mutane batattu. Idan mutane suka yanke kauna to tabbas sun kauce hanyar Allah ne, amma muminai suna ganin hanyar gyara a wartsake, sai dai duniya ba ta sallama wa maganarsu, don haka dole ne wannan faganniya da dimuwa ta ci gaba.
Amma Allah madaukaki ya yanke duk wani uzuri ga dan Adam, kuma ya girmama shi, ya shiryar da shi duk wani tafarki, ya yi masa duk wata falala yana mai cewa: “Hakika mun girmama 'yan Adam, muka dauke su a tudu da kogi, muka arzuta su daga dadada, kuma muka fifita su a kan mafi yawan abubuwan da muka halitta fifitawa. (Isra'i: 70)
Sannan ya fifita shi a kan duk wata halitta kowace iri ce, ya sanya shi mai matsakaicin hali da idan ya ga dama sai ya fi mala’ika, idan kuwa ya ga wata damar sai ya fi duk wata halitta kaskanci. Kuma wannan ruwayar tana nuna mana haka a sarari yayin da take cewa: An karbo daga Imam Sadik (a.s): -yayin da Abdullahi dan Sinan ya tambaye shi Mala'iku ne suka fi ko 'ya'yan Adam?- sai ya ce: "Amirul Muminin Ali dan Abu Dalib ya ce: Ubangiji madaukaki ya sanya wa mala'iku hankali babu sha'awa, ya sanya wa dabbobi sha'awa babu hankali, sai ya sanya wa 'dan Adam duka biyun, to duk wanda hankalinsa ya rinjayi sha'awarsa to shi ya fi mala'ika, kuma duk wanda sha'awarsa ta yi galaba kan hankalinsa to ya fi dabbobi kaskanta. (Biharul Anwar: 60/299/5).
Idan mutum ya samu kamala yana iya zarcewa ya tafi babu iyaka ga kamalarsa domin daga Allah take wanda ba shi da iyaka. Yana iya kasancewa shi kadai ya fi dukkan mutane da sauran halittu daraja kamar yadda yake ga Annabi (s.a.w) da alayensa (a.s). Don haka ne zamu ga wata ruwayar tana nuni da hakan tana mai cewa: Daga Annabi (s.a.w): "Babu abin da ya fi dubunsa daga irinsa sai mutum". (Kanzul Ummal: 34615). Don haka ne zaka ga mutum daya amma ya fi miliyoyin mutane daraja.
Babbar ni’imar da Allah madaukaki ya yi wa mutane shi ne ta rashin toshe musu kofar kamala matukar suna son su samu kamalar. Kuma wannan kofa har su mutu ba a toshe ta, sannan kuma akwai wasu kofofin da ba su da iyaka da suke a bude har bayan mutuwa!.
Sannan akwai abin mamaki ga wannan halitta ta mutum mai sirri maras iyaka, sai dai Allah madaukaki ya yi mana bayani ta hannun annabawansa da wasiyyansu ka n dalilin da ya sanya shi halittar wannan halitta mai ban mamaki.
Ubangiji madaukaki yana cewa: Ban halicci mutun da aljani ba sai don su bauta mini. (Zariyat: 56).
Imam Ali (a.s) ya ce: "An umarce ku da tsoron Allah ne, kuma an halicce ku don kyautatawa da biyayya ne". (Nahajul balaga: Ibn Abil hadid/3/108)
Imam Husain (a.s) ya ce: "Ya ku mutane, Allah mai daukakar ambato bai halicci mutane ba sai don su san shi, idan suka san shi sai su bauta masa, idan suka bauta masa sai su wadatu daga bautar waninsa. Sai wani mutum ya ce: Ya dan manzon Allah (s.a.w), ina fansarka da iyayena, mene ne sanin Allah? Sai ya ce: Sanin kowane mutanen zamani Imaminsu wanda yake wajibi ne su yi masa biyayya". (Biharul Anwar: 23/83/22).
Imam Sadik (a.s) yana cewa: -yayin da wani zindiki ya tambaye shi cewa; saboda me Allah ya halicci halitta alhalin ba ya bukatar su, kuma babu wanda ya tilasta masa kan halitta su, kuma ba ya cancanta ya yi wasa da mu?- "sai Imam (a.s) ya ce: Ya halicce su domin su yi abin da zasu samu rahamar Allah da shi ne, sai ya yi musu rahama". (Biharul Anwar: 10/167/2).
Magana kan wannan lamari tana bukatar rubutu na musamman don haka sai mu kulle ta hakan, sai dai duk da hakan mutum yana da wani rauni maras misali. Duba abin da mahaliccinsa yake cewa: “An halicci mutum mai rauni”. (Nisa'i: 28).
Sannan wasiyyin manzon rahama Muhammad (s.a.w), Imam Ali (a.s) yana cewa: Mutum miskini ne; Ajalinsa boyayye ne, ciwuwwukansa taskace suke, aikinsa kiyayye ne, sauro yana sanya shi zogi, shakewa (kwarewa) tana kashe shi, dan gumi yana sanya shi wari. (Nahajul balaga: Ibn Abil hadid /20/62).
Wannan ruwaya tana nuna mana matukar raunin mutum a cikin samammun bayin da Allah madaukaki ya halitta.
Ya kai dan Adam ka koma ka san matsayinka gun ubangijinka, ka san jagoran zamaninka, domin ka samu tsira gun Allah (s.w.t) daga dukkan kaskanta, ka kuma samu kamalar da ba ta da iyaka a wurinsa!.
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Wednesday, April 07, 2010
Ƙara sabon ra'ayi