Halaye Nagari

 Halaye Nagari

Kyawawan Halaye
Kyawawan D'abi’u
Kyawawan d'abi’u su ne ruhin shari’a, kuma asasin addini, babu wani Annabi da ya zo sai da ya yi kira tsakanin mutane da kyawawan d'abi’u, da kuma tilascin tsarkake su daga abin da yake iya kai su ga aikata munanan d'abi’u, da kuma nesantar da su daga abin da yakan iya lalata hadafinta, sai ya zana mana tafarki da hanya, ya gina mana dokoki da zamu yi amfani da su domin kawo canji ga mutum zuwa ga mafi kamalar samuwa wacce mutum zai dogara da ita domin ya kai ga matsayi mai girma na kyawawan halayen, ya kuma zamanto daga zab'ab'b'u tsarkaka daga bayinsa.
Ilmin Kyawawan D'abi’u
Ilmin kyawawan d'abi’u ilmi ne da yake da ma’auni da za a iya dogara da shi, shi ne tattararrun dokoki da ya kamata dabi’ar d'an Adam ta kasance a kanta bisa wad'annan dokokin kamar yadda aka gindaya a zance ko a aiki ko a zuciya. Da wad'annan ma’aunai zamu zana hanyar kyawawan d'abi’u abin yabo, mu kuma yi k'ok'arin iyakance hadafinsu da abubuwan da suka ginu a kan su.

Kyawawan D'abi’un Musulunci
D'abi’un musulunci su ne tattararrun zantuttuka da ayyuka na zahiri da na bad'ini da suka d'oru bisa ka’idoji, da kuma ayyuka mad'aukaka da ladubban da suka d'oru a kansu, wad'anda suka dogara a kan ak'ida da shari’ar musulunci da dogaro mai k'arfi daga kur’ani mai girma da sunnar Manzon Allah (S.A.W) da imamai tsarkaka (A.S). Kyawawan d'abi’u a musulunci ba komai ba ne sai b'angare na addini, kai shi ne k'ashin baya da ruhin addini ma[1][1].

Hadafin Kyawawan D'abi’u
Hadafin kywawan d'abi’u shi ne kare ayyukan mutum, na zahiri da na bad'ininsa da kuma tsarkake tunaninsa da samuwarsa daga karkacewa; wato hadafin shi ne samar da mutum ko kuma al’ummar da take takawa zuwa ga kamala, ta kuma tsayar da adalci, da rik'on amana, da taimakekeniya, da kuma kama hannun juna domin kare rayuwar al’umma daga fad'awa cikin fasadi da zalunci da sauran miyagun al’adu da d'abi’u.
Da lizimtar kyawawan d'abi’u ne mutum ko al’umma zata samu kariya daga karkacewa da kuma lizimtar tafarkin shiriya na gaskiya. Hadafin ilimin kywawan d'abi’u bai tak'aita a kan daidaikun mutane kawai ba, ya had'a har da al’ummu da jama’u daban-daban, ta yadda kyawawan d'abi’u zasu mamaye rayuwarta da siffofinta domin kai wa ga mafi daukakar ci gabanta.
Wani baiti yana cewa:
Al’umma kawai ita ce kyawawan dabi’unta matuk'ar ta wanzu.
Idan kuwa al’umma ta kau to kyawawan dabi’unta ne suka kau.

Madogarar Asasin Kyawawan D'abi’u
Kafin mu yi magana kan asasin akhlak' na musulunci zamu yi nuni zuwa ga cewa akwai abubuwa da yawa wad'anda suke madogarar asasin kyawawan d'abi’u, daga ciki akwai:
- Zuciyar mutum wacce take tunkud'a shi zuwa tafarkin alheri, kuma take hana shi aikata sharri da mummuna.
-Dabi’ar zuciya da take tunkud'a mutum zuwa ga sadaukar da dukkan maslaharsa saboda maslahar mutane.
-Hankali da yake son kamala, ya ke kuma riskar mummuna da kyakkyawa a aikace.

Dangane da akhlak' na musulunci muna ganin yana da manyan madogara na asasi guda biyu manya, su ne:
1- Hankali
2- Annabin rahama (S.A.W) da Ahlul baiti (A.S)

1- Hankali
Hankali; Ana auna ayyuka da hankali ne, kuma da shi ne mutum yakan kai zuwa ga sa’ada da kamalar rayuwa ta lahira, da hankali ne muke riskar dalilin halitta, da kuma riskar abubuwa masu daraja, muke kuma k'ok'ari zuwa ga mafi kyau ma fi wanzuwa, da shi ne muke neman tafarkin sani, da hanyoyin ibada, Imam Assadik' (A.S) ya ce: “Mafi kamalar mutane hankali shi ne mafi kyawunsu d'abi’a”[2][2].
Dogaro da wannan hadisin muna iya cewa; hankali na aiki shi ne abin nufi, ba hankali na nazari ba, in Allah ya yarda idan na kammala littafina wanda yake magana kan kashe-kashen hankali da matsayin kowanne, to a nan mun kawo bayani game da hankali dalla-dalla.
Hankali a nazarinmu shi ne madogara ta asali na kyawawan d'abi’u, idan aka rasa shi sai dabi’ar halin dabbanci ta mamaye mutum.

2- Annabi Mai Girma Da Ahlul Bait (A.S)
Annabi mai girma ya zo ne domin ya tsarkake mu ya cika mana kyawawan d'abi’u yayin da yace: “Kawai an aiko ni ne domin in cika kyawawan d'abi’u”[3][3].
Shi ne mafi kamalar mutane, kuma babu wani daga halittu da ya kai inda ya kai, shi ya sanya ubangiji mad'aukaki ya fad'a yana mai yabonsa: “Lallai kai kana kan halayen d'abi’u masu grima ne”[4][4].
Abin da ya hau kanmu shi ne mu yi rik'o da kyawawan dabi’unsa, mu yi koyi da shi domin shi ne abin koyi kuma madogara garemu a kyawawan d'abi’u, har ma a kowane fage.
Amma Ahlul Baiti (A.S) su ne wad'anda suka gaji ilimn annabawa da na k'arshensu Muhammad (S.A.W), kuma mutane sun gani kuma sun ji kyawawan d'abi’un alayensa (A.S) wancce take iya tuna musu kyawawan d'abi’unsa (S.A.W). Da sannu zamu ambaci wasu daga kyawawan dabi’unsu a wannan littafin namu;
Daga ciki;
“Ya zo cewa imam Hasan da Husain (A.S) sun wuce wani tsoho yana alwala bai iya ba, sai suka yi kamar suna ‘yar jayayya a kan cewa; wanene yafi iya alwala a cikinsu, wannan kuwa sun yi haka ne domin su koya masa yadda ake yin alwala, sai kowanne ya ce kai ne ba ka k'ware ba sosai, sai suka ce: ya kai wannan tsoho yi mana hukunci, sai kowannensu ya yi alwala sannan sai suka ce: Waye a cikinmu ya fi iyawa? Sai ya ce: Ai duk kun iya alwala, sai dai wannan tsoho jahili shi ne bai iya ba, yanzu kam ya koya daga gareku”[5][5].
Lura da yadda Ahlul Bait (A.S) suka shiryar da wannan tsoho domin ya zama mana darasi a wajan yadda ake mu’amala tare da manyan mutane.
[1] Akhlak' wal adabul islamiyya: 8.
[2] - Usulul kafi: kitabul akal wal jahal; H: 7.
[3] - Makarimul akhlak':3. Biharul anwar: 16/210.[4][4] - Al-kalam; 4.[5][5] - Biharul anwar: 43/319
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation

Ƙara sabon ra'ayi