Ilimin Gaibi

Ilimin Gaibi

Me ake nufi da Ilimin Gaibi?
Kafin bayar da amsa yana da kyau mu san me ake nufi da gaibi domin amsar ma'anar sanin gaibi ta fito a fili. A cikin littattafai ya zo cewa; Gaibi shi ne duk wani abu da ya boya ga mutum. Kitabul Ain: Khalil Farahidi; 4/454, Lisanul Arab: 1/654, Majma’ul Bahrain: 2/134.
Don haka muna ganin gaibi shi ne abin da ya boyu daga gabobinmu da muke riskar abubuwa da su, wadanda muke kiran su da "Mariskai", wadannan mariskar sun hada da ji, da gani, da lasa, da shafa, da shaka. Sai dai a cikin Kur'ani mai girma an yi amfani da kalmar Gaibi ga dukkan abin da yake ba mahalarci ba ne. kamar yadda ya zo a cikin Surar An’am: 73.
Da kuma fadinsa: "Masanin gaibi da sarari, kuma shi ne mai hikima mai masaniya". Kamar yadda ya zo a surar Tauba: 94, da 105.
Domin lamarin mas'alar gaibi ya bayyana garemu sosai ya zama wajibi mu yi duba zuwa ga kashe-kashen gaibi; idan mun duba zamu ga gaibi ya kasu gida biyu: Sakakken gaibi, da Gaibin dangantaka. Sakakken gaibi; Shi ne gaibin da yake sake ba kaidi, wanda yake babu wani wanda ya san shi sai mahaliccin duka, kuma babu wata hanya da za a iya saninsa, irin wannan gaibin ya hada da sanin zatin Allah madaukaki, da sanin hakikanin siffofinsa da sauransu. Amma Gaibin danganta; Shi gaibi ne wanda saninsa ya danganta da matsayin ilimin mai saninsa da kusancinsa da mabubbugar gaibi duka wato; Allah mahalicci. Yana buda wa bayinsa saninsa daidai gwargwadon yardarsa da su, da karfin dauke sakonsa da suke da shi, da kuma zamani ko wurin da zai ba su wannan sanin na gaibi, kuma ya yi nuni da hakan a cikin surar Jinni: 26-28.
Da wannan ne wani abin yake zama gaibi dangane da wani mutum, amma ba gaibi ba ne dangane da wani, sai aka ambace shi Gaibin dangantaka. Sai wani abu ya kasance gaibi ga mariskai amma bai gaibi ba ne ga hankali; mariskai ba sa iya riskar dokoki gama-gari, sai dai suna riskar daidaikun halittun da ake iya riskar su a fili ta hanyoyi mabambanta kamar ji, da gani, da shaka, da tabawa. Haka nan ma abin da yake cikin gida ba gaibi ba ne ga wanda yake cikinsu, amma gaibi ne ga wanda yake wajen gidan. Sai wani abu ya kasance gaibi gun mutane amma ba gaibi ba ne gun wasu dabbobi, ko aljanu, ko mala'iku; musamman zamu ga akwai wasu dabbobi da suke iya gani ko jin wasu sauti da dan Adam ba ya iyawa. Haka nan wani abin yake gaibi a wurin dukkan halittun Allah, amma babu wani abu da yake gaibi a wurin Allah madaukaki, domin shi ne ainihin ilimi.

Shin Akwai Wanda Ya San Gaibi Ban Da Allah?
Idan muka duba ayoyin Kur'ani mai girma zamu ga suna nuna mana sanin gaibi da ma abin da yake sarari duk na Allah ne; ayoyi kamar: Naml: 65, da An’am: 59. Sai dai idan mun lura zamu ga sanin gaibi da ma'anar da ya zo a wannan ayoyin bai kore samuwar saninsa ga wasu bayi da Allah ya zaba ba, don haka ne zamu iya fahimtar ma'anar babu wanda ya san gaibi sai Allah tana nufin asalin saninsa, da cewa; babu wanda ya san gaibi da kansa sai ubangiji madaukaki. Amma wanin ubangiji idan ya san gaibi to da sanarwar ubangiji ne ba da kansa ba, don haka saninsa da gaibi yana bin sanarwar da Allah ya yi masa ne, da ba shi kyautar wannan ilimi da Ubangiji madaukaki ya yi, don haka ne zamu ga ayar nan ta surar Jinn: 26-28, da sauran ayoyi kamar: Aali Imran: 179, 44, da Yusuf: 102, duk suna nuni da haka.
A cikin Kur'ani mai girma ya zo da bayanin annabawa (a.s) da Allah madaukaki ya sanar da su gaibi, idan mun koma wa ayoyi kamar haka: Yusuf: 41, da Aali Imran: 49, zamu ga yadda annabawa suka san gaibi kuma suka gaya wa mutane shi. Kamar yadda zamu samu labarun fadin abubuwan da zasu wakana da imam Ali (a.s) da sauran imamai (a.s) suka yi, kamar yadda ya zo a cikin Nahajul Balaga: 186, An’am: 75, da Kafi: 1/257. Sai dai sun sanar da mutane cewa; wannan duk daga koyarwar manzon Allah (s.a.w) da ya sanar da su, wato; ba sun sani ba ne su a kashin kansu, sai dai sanarwa ce daga Allah da manzonsa.
Hafiz muhamad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Thursday, September 24, 2009

Ƙara sabon ra'ayi