DALILAN DA SUKA ALI YA YI SHIRU

DALILAN DA SUKA ALI YA YI SHIRU

            Sanin kowa ne cewa Annabi (saww) bai bar duniya ba sai da ya nada wanda zai gaje shi a bayansa, wannan magajin nasa kuwa shi ne imam Ali dan Abu Dalib (as), amma abin tambaya shi ne mene ne ya sanya bayan wasu sun hau wannan kujera ta khalifanci sai Imam Ali (as) ya kyalesu?

Amsar ita ce: lokacin da annabi (saww) ya yi wafati ya bar mutane da yawa wadanda suke sababbin shiga musulunci ne, don haka ba su da wadataccen sani a kan musulunci, su kuma wadanda suke rike da madafun iko sun dau alwashin sa kafar wando daya da duk abin da zai rabasu da wannan mulki, don haka dawo da ragamar iko zuwa ga ma'abocinta zai janyo mummunan yakin da zai sanya da yawa su koma shirka su bar musulunci, don haka imama Ali (as) ya zabi ya hakura don kiyaye imanin musulmi.

Haka nan dai daga cikin dalilai shi ne cewa Imam Ali (as) ya san cewa manyan kasashen duniya na wancan lokaci kamar Rum da Farisa suna nan suna neman kafar da za zu afkawa musulmi, don haka yin rikici a wannan lokaci zai ba su damar kawar da msuslunci gabadaya.

Sannan a bangare guda ga munafikai da suka yi kwanton bauna don samun damar da za su hambarar da musulunci.         

AttachmentSize
File 13109.f.hoosa_.mp434.57 MB

Ƙara sabon ra'ayi