ISRAI'ILA DA IRAN
Tun bayan cin nasar juyin juya halin musulunci da ya wakana a kasar iran sai haramtacciyar kasar Isra'ila ta daura damar yin gaba da ita, da kuma daukar duk wani mtaki da zai iya kaita zuwa ga rushewar wannan tsari na musulunci, kafin dai cin nasarar wannan juyi a lokacin hambararren sarki Sha , Isra'ila ta kasance babbar kawar Iran, amma bayan cin nasarar juyin musulunci a kasar sai wannan kasa ta musulunci ta yanke alaka da haramtacciyar kasar Isra'ila, inda ta maye gurbinta da halatattun masu kasa wato paalatsinawa.
Sanin kowa ne ita dai kasar Patsino ba mallakar Yahudawa bace, amma saboda fin karfi sakamakon taimakon turawa musamman na Ingila aka afkawa wannan kasa ta Palatsino da yake, aka tsugunar da Yahudawa a wannan kasa inda suka yi kakagida suka kwacewa Palatsina kasarsu kuma suke kashesu a kowace rana.
Attachment | Size |
---|---|
13103.f.hoosa_.mp4 | 30.97 MB |
Ƙara sabon ra'ayi