Mene ne munufar guyin musulunci

Mene ne munufar guyin musulunci

Allah ya sanya musulunci ya zama addini kuma bai yardarm mu bi wani addini ba kowa bayan musulunci.

          Musulunci ya tanadar mana da duk wani abu da muke bukata a duniya da lahira, wato ba kawai yana dauke da skon sallah da azumi da sauransu bane, lallai yana tsara mana yadda za a yi mulki, da kuma siyasarsa a musulunci, ashe za muga cewa wadanda suke cewa; musulunci daban siyasa daban suna karyata alkur’ani da sunna ne, domin idan muka ga a cikin Alkur’ani mai girma akwai ayoyi sama da 6000 amma ayoyin da suka yi Magana a kan hukunce-hukuncen fikihu basu wuce 500, mafi yawancinsu suna Magana ne a kan harkokin yau d kullum da ya yadda za a gudanar da al’amuran al’umma.

Sannan Annabi (saww) ya aikata hakan, inda ya yi gwagwarmayar ya kafa gwamnatin muslunci, wannan kuma shi ne abin da ya bar al’umma a kai.

Kafa gwanatin musulunci shi ne kawai zai iya kare hakkokin kowa da kowa idan har an aikata shi yadda yake.

AttachmentSize
File 13090.f.hoosa_.mp435.96 MB

Ƙara sabon ra'ayi