HAƘIƘAR SHI'A (4)

HAƘIƘAR SHI'A (4)

Kafin mu shiga cikin bayanin ma’anar wannan kalmar shi’a a harshen larabci da kuma isɗilahi ya zama wajibi mu ɗan  yi shimifɗa da wasu bayanai waɗanda suna da tasri sosai wajan fahimtar duk a bin da za mu ambata a nan gaba, shimfiɗar ita ce kamar haka:

Mas’ala ta farko: Musulunci da musulmi

A cikin wannan fasali zan kawo ta’arifin musulunci imani, da kuma wanene musulmi sakamakon muwuyacin halin da muke cike  na waɗnsu suna kafirta, musulmi suna halarta jininsa, irin wannan musifa da ta afka a kan musulmin duniya tana janyo mummuna ɓarna da munana fuskar musulunci  a wajan shi kansa musulmin wanda bai yi karatu ya san haƙiƙanin musulunci ba kokuma ba shi da kyakkyawar aƙida, wanda kuma ba musulmi bane to an sanya masa mummunar kyamar musulmi da musulunci ta yadda a wannan zamani namu daga ka ji an ce masu kishin musulunci to abin da kwakwalwarka za ta kawo shi ne zubar da jinida ta’addanci, wannan kuwa ba wani abu ne ya janyo haka sai ƙulle- ƙulle da makirci na tura da kasashen yammacin duniya inda suke, horar da mutane da sunnan musulmi kuma ake basu wani karatu wanda ko kaɗan bai shi da alaƙa da koywarwa musulunci, wanda ko da ma ba mu kawo wasu dalilai masu yawa ba wannan aya ta Alƙur’ani mai girma ta ishe mu mu san duk wani wanda ya tashi da sunan musulunci yana kashe mutane ko ya na kafirta su kokuma yana cin zarafinsu, to tabbas wannan turwa maƙiya addinin musulunci yake yi wa aiki waɗanda suka kutso ta cikin musulmi suna ta rusa musulunci ta cikinsa, sannan Allah da manzon Allah sun barranta daga gareshi, shima kuma ya barranta daga Allah da manzonsa, Allah yana cewa, don haka mai karatu ka karanta ka gani shin menene muslunci, kuma wanene musulmi ? .

 

AttachmentSize
File 12067-f-hoosa.mp447.7 MB

Ƙara sabon ra'ayi