SHAHADAR SAYYIDA FAƊIMA (AS) (14)

SHAHADAR SAYYIDA FAƊIMA (AS) (14)

KWACE FADAK

Bayan dukan sayyida Faɗima (as) wanda wannan dukan ya sanya ta yi ɓarin cikin da take ɗauke da shi, wanda aka sanaya wannan ɗan da ta yi ɓari Muhsin, sai aka kwace mata Fadak, ita dai gona ce wannce Annabi (saww) ya yi8 sulhu da yahudawa suka bar masa.

Fadak ba gado bace tun Annabi (saw) yana da rai ya mallakawa sayyida Faɗima, sakamakon unmarnin da Allah a ya yi msa na ya bawa makusantasa haƙƙinsu

 (وآت ذا القربى حقه)

Bayan saukar wannan ayar sai annabi (saww ya baiwa sayyida Fadak, tun daga wannan lokaci Fadak ta zama mallakar sayyida Faɗima  kuma ta kasance a hannunta har Annabi (saww) ya yi wafati bata gushi ba tana hannunta, amma yan yin wafati sai aka kori duk ma’aikatanta waɗand suke a ciki.

Sayyida ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sai ta fara fafutukar dawo da haƙƙinta in da ta tambayi Abubakar da ya bata gonarta, shi kuma sai ya hanata ya dage yana cewa Annabi (saww) yana cewa mu annabawa ba’a gadarmu abin da muka bari sadaka ne.

Sayyida Faɗima (as) ta bashi amsar wannan maganar, inda ta bayyana masa cewa: shin ya fi annabi sani ne, kokuma ya fi imam Ali sani, kokuma ya fita sani, lallai wannan ba hukuncin Allah bane, domin Allah ya raba gado ya baiwa kowa yayan annanbawa sun gaji iyayensu annanbawa, kamar yada ayoyin alƙur’ani da yawa suk ayi bayin haka shi kuwa annabi yana aikata alƙur’ani ne, somin ayikata umarnin alƙur’ani shi ne bin umar Allah

AttachmentSize
File 11433-f-hoosa.mp432.73 MB

Ƙara sabon ra'ayi