Auren Mace Sama da Daya

Auren mace sama da daya ya zo a cikin shari'ar musulunci don rage yawan auren mata barkatai da musulunci ya tarar ana yi a wancan lokacin ta yadda namiji daya zai auri kusan mata goma ko kasa da haka ko ma sama da hakan. Sai musulunci ya zo ya kayyade shi da guda hudu kawai, sai dai ya sanya sharadin adalci ga wanda zai auri sama da mace daya, idan kuwa ba zai iya adalci ba to wajibi ne kansa ya auri guda daya tal. Adalci a nan yana nufin adalcin tafiyar da rayuwarsu da mu'amala da su bisa daidaitu ba tare da karkata zuwa ga dayar ba ko nuna wa wata wariya ba.

AttachmentSize
File abfab5076dc34a57c1f632875db47a3c.mp414.12 MB

Ƙara sabon ra'ayi