Ibn Taimiyya da tahidi Ya ƙirƙiri ya sabon tauhidi

Tauhidin da Ibn Taimiya  yake ta kafirta mutane a kansa ba shi ne tauhidin da Annabi Muhammad ( saww) yazo da shi ba, tauhidin da manzon Allah (saww) yazo da shi shi ne wanda Imam Ali da Sayyida Faɗima(as) take a kansa, saboda su ne waɗanda Allah da manzonsa suka ce a bi, kamar yadda Annabi (saww) yake cewa: na bar muku nauyaye guda biyu waɗanda ba za ku bata ɓayana idan har kun yi riƙo da su, su ne littafin Allah da kuma ahalin gidana... amma abin baƙin ciki a yau idan mutum ya nuna wilayarsa garesu sai wahabiyawa su kafirtashi, duk da cewa tauhidin da suke a kansa tauhidi da ya saɓa da tauhidin da musulmin duniya suke a kansa, kamar yadda suke cewa: Allah yana sama yana zaune a kan al’arshi, kuma duk wand a bai yadda Allah yana sama to kafiri ne, sakamakon gurɓatacciyar fassara da suke yiwa wasu ayoyi da hadisai. 

AttachmentSize
File f0cfd1aa46420797f42d1865be5ba913.mp420.15 MB

Ƙara sabon ra'ayi