ANNABTA (4)

Wani mutum ya tambayi Imam Sadiƙ (as) cewa:(( ta ina zan tabbatar da annabawa da manzanni?))Sai imam Sadiƙ (as) ya amsa da cewa:       Haƙiƙa mu yayin da muka tabbatar cewa muna da mahalicci wanda yake maɗaukaki a garemu, da kuma duk sauran ababan halitta.
Ya yin da wannan mahaliccin ya kasance mai hikima, maɗaukaki, ba zai yi wu wani a cikin ababan halittarsa ya iya ganinsa ba, ba za su iya taɓa shi ba, ballantana su taɓa jikinsa shima ya taɓa jikinsu, Su kafa masa hujja, shima ya kafa musu hujja, sai ya tanbbata cewa yana da jakadu a cikin halittarsa.
((Suna faɗar saƙo daga gareshi izuwa ga bayinsa, kuma suna shiryar da su izuwa abin da masalahaarsu take ciki, da kuma abinda amfanisu yake ciki, da kuma abin da wanzuwarsu take ciki, , wanda idan suka barshi, to halakarsu da ƙarewarsu tana ciki, sai ya tabbata cewa akwai masu umarni da hani  daga cikin bayi, daga ubangiji mai hikima kuma masani, masu kawo saƙonsa mai girma da ɗaukaka, su ne annabawa)).

AttachmentSize
File fc9a0ba0ef56d785572b5e6cf09377ae.mp416.14 MB

Ƙara sabon ra'ayi