Tauhidin Ibn Taimiyya ya yi karo da tauhidin Ahlul Baiti (12)
Yadda Ibn Taimiyya ya kasa Tauhidi ya saɓa da haƙiƙanin abin da haƙiƙanin yadda masu bauta suke, koma wace irin bauta ce, domin duk wanda yake bauta wani abu to yana bauta masa ne don ya yi imani da cewa wannan abin shine rabbu wato mai gudanar da al’amuransa, kuma shi ne yake da ikon amfanar da shi kokuma cutar da shi, don haka ba a taɓa samun cewa ga wani ya yarda ga wanda yake gudanar da al’amuransa amma yana bautawa wani ba, bilhasili ma mutane suna bautawa abin da suka yi imani da cewa shi ne yake iya cutar da su kokuma amfana da su, amma kuwa da suka san cewa ba shi da ikon ya cutar da su kokuma amfanar da su to babu ruwansu da shi ballantana ma su bauta masa
Attachment | Size |
---|---|
2d0da213ca37e43bb337b15eb96070b0.mp4 | 21.77 MB |
Ƙara sabon ra'ayi