TARIHIN IMAM HUSAIN( AS) 17

Imam Husain ya fita daga maka ya nufi hanyarsa ta zuwa birnin Kufa, sakamakon kasantuwa Banu umayya suna nemn yi masa kisan mummuke, ta yadda suka yan leken asirin a ko’ina, suna bibiyar imam Husain duk inda ya yi don su kasheshi, don haka ita Maka ta kasance waje mai hadari a tare dashi, saboda kamar yadda ya kasance bashi da mataimaka a madina haka ya kasance bashi da mataimaka a Maka.
Yana da kyau mu fahimci cewa maka ta kasance tana kunshe da gida je na kabilu daban – daban wadanda ake kira banu wane banu – wane, yawansu ya kai kimanin 25, daga cikinsu akwai Banu Umayya, da Banu Abduddari, da makamantansu, kuma mafi yawan wadannan gida- gida sun kasance suna tsananin gaba da imam Aliyyu dan Abu Dalib (as) da kuma sauran Ahlul baiti sakamakon kasantuwar imam Aliyyu shi ne sarkin yakin Annabi (saww), shi ne ya kashe manyan kafiran maka a yayin da aka yi yakin badar da uhudu da sauran ya kokin da Allah ya daukaka musulunci dasu, wannan shi ne babban dalilin da ya sa suke tsananin gaba dashi, kuma su ka dauki alwashin daukar fansar wadannan kafirain kakanninsu da yan uwansu, wadannan ce ma ta sa Mu’awiya dan Abu Sufyan ya dauki mummunar kiyayya da imam Aliyyu (as), sannan dansa Yazidu ya gaji wannan gaba har ta kai ya yi umarni da kasha imam Husain.
 

AttachmentSize
File 6560418b16e04d07f3da6f3957392446.mp420.7 MB

Ƙara sabon ra'ayi