Ibn Taimiyya da tauhid Siffofin Allah

Kamar yadda a can baya ibn Taimiyya yake da aƙidar da saɓawa aƙidar da musulmi suke a kai a kan a binda ya shafi al’arshi, haka nan a  nan ma ya saɓa dasu a kan siffoin Allah (t) in inda ya tafi a kan cewa duk wata siffa da ta zo a cikin Alƙur’ani mai girma, ko kuma a wata riwaya to dole ne a ɗauketa da gundarin ma’anarta ta harshen larabaci, ba tare da an fassara ta da abin da ya dace da hankali ba, kuma ba tare da an dubi matsayin zatin Allah ba, na cewa akwai abin da idan aka fassara shi kamar yadda Ibn Taimiyya yake nufi to babu shakka hakan zai zama an jingina naƙasu Allah, kamar magana akan hannu, fuska,, ciki, da makamantansu.
Wannan guɓatacciyar aƙida ta Ibn Taimiyya ta sanya ya ce: Allah yana da hannu irin dai wanda muka sani, kuma yana da fuska kamar dai yadda aka san menene fuska,  

AttachmentSize
File c863e05f5e3baa9626a43f5dd26ffe14.mp422.45 MB

Ƙara sabon ra'ayi