TARIHIN IMAM HUSAIN( AS) 15

 
Bayan Annabi (saww) ya yi wafati al’umma ta juyawa iyalan gidan Annabi (saww) baya, sakamakon kin bin umarnin da Annabi (saww) ya yi na abi iyalan gidansa, amma duk da haka imam Ali ya yi hakuri.
A na zaɓar imam Ali a matsayin khalifa bayan mutuwar Usman sai aka yi masa ca ana yaƙarsa, Mu’awaiya ɗan Abu sufyan da danginsa banu Umayya su ne waɗanda suka fi tsananta gaba da Annabi (saww) iyalan gidansa (saww), don haka ne suka ƙarar da rayuwarsu wajan yaƙar Annabi (saww), sannan bayan imam Ali ya karɓi halifanci sai suka ƙara fito da wannan gaba.
Bayan imam Ali(as) ya yi shahada imam Hasan ya yi sulhu da mu’awiya daga cikin sharuɗan da ka yi sulhu a kansu shi ne: idan zai mutu kada ya naɗa wani a matsayin mai jiran gado, a kyale al’ummar musulmi su zaɓi wanda suka ga ya dace ya zama khalifan musulmi, amma abin takaici Mu’awiya bai cika wannan alƙawari ba sai ya naɗa ɗansa Yazidu a matsayin halifa, kuma ya yi masa nuni da cewa babu wanda yake gani a matsayin barazana a kan wannan mulki na Yazidu kamar imam Husaini don haka ya tusasahi da ya yi masa mubaya’a, shi kuwa ima Husaini ko kaɗan bai yarda da haka, saboda na farko dai shi Husain yana daga cikin khalifofin da Annabi ya yi umarni da a bisu, ga Yazi du fajiri ne kuma fasiƙi, don haka ya haramta ga duk wani musulmi ya yi biyayya gareshi  matsayin sugaba.

AttachmentSize
File acb422f95b6909be2f66120fe5f30c69.mp419.5 MB

Ƙara sabon ra'ayi