ANNABTA (15)

Allah ya aiko Annabi Muhammad (saww) don ya zama rahama ga talikai, sannan ya umarceshi ya yi kiran mutane izuwa ga ubangijinsa da hikima da kuma wa’azi mai kyau.
A bisa wannan ne za muga cewa; Annabi (saww) ya koywar da al’umma kyawawan ɗabi’u , kamar tausayi, jinƙai, da h idimtawa al’umma.
Annabi baya tilastawa wani a kan ya shiga musulunci, bilhasili ma waɗanda ba sa son su shiga musulunci suna iya zama a kasar musulmi, ba tare da wani ya tsangwamesu ba, sai dai kawai abin da ake buƙata a wajansu su kula da, duk wajibobin da suke kansu, kuma kada su yaƙi musulmi.
Amma abin takaici a wannan zamani wasu suna nuna musulunci amatsayin wani addini na ta’addanci, da zub da jinanen waɗanda ba su ji bakuma ba su gani ba, suna kashe waɗanda ba musulmiba, haka siddan, haka nan musulman ma ba su tisara ba, suna kafirta su kuma suna kashe su, to lallai wannan aƙida ba musulunci ba ce. 

AttachmentSize
File e76cc0dce2c0198bea4382cbf4890142.mp418.95 MB

Ƙara sabon ra'ayi