SHAHADAR SAYYIDA FADIMA (AS) (5)
Kafin Annabi (saww) ya yi wafati kowa ya sani ƙarara cewa Manzon Allah (saww) ya naɗa Amirul Muminina Aliyyu Ɗan Abu Ɗalib a matsayin halifansa.
An rawaito cewa ranar goma sha takwas 18 gawatan zulhijja manzon Allah (saww) ya isa izuwa wni waje wanda ake kira da suna Gadir khum, Gadir ya nufin kudiddifi wato wajan da ruwa yake taruwa shi kuma ƙhum sunan wajan kenan, wato kudiddifin ƙhum, bayan ma’aikin Allah ya isa wannan waje wanda kowa ya sani cewa aikinsa yana yi ne bisa yadda Allah ya yi masa umarni sai Allah ya sake saukar masa da aya cewa:
)يا ايها الرسول بلغ ما انزل اليك من ربك فان لم تفعل فما بلغت رسالته و الله يعصمك من الناس(
( ya kai wannan manzo ka isar da abin da aka sauka maka daga ubangijinka idan kuma ba ka aikata hakan ba to baka isar da saƙon Allah ba , kuma Allah zai kareka daga mutane))
Don haka sai manzon Allah(saww) ya tattara mutane ya ce: waanda ya iso wannan waje ya tsaya wanda kuma bai ƙaraso ba a yi jiransa ya zo, sannan ya yi umarni da shirya masa wajen a ƙarƙashin bishiyoyi, a cire ƙayoyi, a kawar da duwastu, sannan a ka yi kiran sallar azahar , aka yi sallar, wannan ranan ta kasance mai tsananin zafin rana har mutane sun kasance suna sanya mayafansu a ƙarƙashin ƙafafuwansu, wasu kuma suna lulluɓe kawunansu daga zafin rana, bayan an idar da salla sai ma’aikin Allah ya hau kan sirdin raƙumai inda ya sa aka haɗa sirdukan a kan rakuma ya zama tamkar wani mimbari ta yadda na nesa za su iya kallonsu, sai ya hau ya yi musu huɗuba, a wannan lokaci kowa ya ji khuɗubar tasa domin wasu suna ɗaga murya suna maimaita abin da yake faɗa domin na nesa ya ji, sai ya fara khuɗubar tasa yana mai cewa:
((...Haƙiƙa Allah mai tausayi masani ya bani labarin cewa: an kusa a yi kirana ni kuma na amsa, haƙiƙa ni abin tambaya ne haka kuma ababan tambaya ne, to idan aka tambaye gobe ƙiyama mai za ku ce?
...Sannan ya ce da mutane su kasance shedu a kan abin da yake faɗa sannan ya ce shin bakwa ji ? sai suka ce muna jinka ya ma’aikinka
Sannan ya ce, haƙiƙa zan kasance bakiin tafki a ranar alƙiyama ina jiranku, ku kuma za ku zo wannan tafkin, faɗinsa ya kai nisan tsakani San’a da Basara, akwai kofuna na azurfa a ciknsa yawansu ya kai adadin taurari, ku duba ku gani ta yaya za ku saɓa mini a cikin saƙalaini (nauyaye guda biyu) sai wani mai kira ya yi kira ya ce ; menene saƙalaini?
Sai Manzon Allah (saww) yac: nauyi mafigirma shi ne Alƙurani, gefensa yana hannun Allah mai firma da buwaya, ɗaya gefen kuma yana hannunku, ku yi riko da shi ba za ku ɓace ba, ɗayan kuma shi ne ƙaramin nauyin wato Ahlul baiti, haƙiƙa Allah mai luɗufi da masni ya bani labarin cewa ku: su waɗannan nauyaye guda biyu ba za su taɓa rabuwa har abada har sai sun zo sun sameni a bakin wannan tafki, sai naroƙi hakan daga ubangiji na, don haka kada ku shige gabansu, sai ku halaka, nkada ku taƙaita a garesu sai ku halaka.
Attachment | Size |
---|---|
32d8b0eceeafd2e0d27b2067225d293c.mp4 | 19.33 MB |
Ƙara sabon ra'ayi