SHAHADAR SAYYIDA FADIMA (AS) (3)
Ya zo a cikin littattafai da dama na malaman Ahlussuna da na mabiya makarantar Ahlul Baiti (as) daga cikinsu littafin Musnad na Ahmad Bin Hambal juzu'I na biyu shafi na 442, da Biharurl anwar juzu'I na 43, Babin tarihin Sayyida Zahra (as) shafi na 131-132.
<نظر النبي ( صلى الله عليه وآله ) إلى عليًّ وفاطمة والحسن والحسين ، فقال : " أنا حرب لمن حاربكم وسلم لمن سالمكم ". مسند ابن حنبل/ج 2/ص 442، و بحار الانوار، ج43، «تاريخ الزهراء» ص 131-132
Manzon Allah (saww) ya yi duba izuwa Ali da faɗima, da Hasan, da Husaini, sai ya ce:
(Haƙiƙ Ni mai yaƙine da wanda ya yi yaƙi da ku, kuma mai lumana ne da wanda ya yi lumana da ku)
Faɗima tsoka ce daga jikin Annabi:
Ya zo a cikin Littafin Sahihul Bukhari Babin manaƙibi alir rasul hadisi lamba ta 3714 cewa:
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - قَالَ « فَاطِمَةُ بَضْعَةٌ مِنِّى ، فَمَنْ أَغْضَبَهَا أَغْضَبَنِى صحیح البخاری باب مناقب آل الرسول (ص) رقم الحديث 3714.
Haƙiƙa Manzon Allah (saww) ya c: ( Faɗima tsoka ce daga jikina don haka wanda ya fusatata (ya ɓata mata) to haƙiƙa ya fusata ni).
Attachment | Size |
---|---|
95082c9193b368e68498a9060b07786b.mp4 | 29.49 MB |
Ƙara sabon ra'ayi