SHAHADAR SAYYIDA FADIMA (AS) (12)
Buhari ya raito a cikin littafin Wato sahihul Buhari, da kuma muslim shima a cikin sahihu Muslim, a cikin babin rashin lafiyar Annabi (saww) cewa: Abudllahi dan Abbas yana cewa: Yayin da Annabi ya kwanta rashin lafiya - wacce daga ita ne ya yi wafati, ya koma ga rahamar Allah- sai ya ce da sahabban da suke tare da shi a wannan lokaci: ku kawo min abin rubutu zan rubuta muku abin da za ku taba bacewa a bayana, sai suka kama hayaniya a gabansa wasu suna cewa; a bashi mana ya rubuta, wasu kuma suna cewa ba za a bashi, sai Umar dan Khaddabi ya ce: Annabi sambatu yake yi, ku rabu da shi littafin Allah ya ishe mu, yayin da sukai ta saɓani da husuma a wajan Annabi, sai Annabi (saww) ya ce: ku ta shi ku rabu da ni.
A taƙaice dai wannan shi ne abin da ya kasance suka hana shi abin rubutu
Babu shakka sun fahimce cewa zai rubuta musu wannan wasiyya ta nada imam Ali a ranar gadir, saboda tun a wancan lokaci ya ce musu: na bar muku abin da ba za ku taba bacewa ba a bayana mutukar kunyi riko da su, sune littafin Allah da kuma iyalan gidana, sannan kuma ya daga hannun imam Ali ya ce: duk wanda na kasance shugabansa to daga yau Ali ne shubansa.
Attachment | Size |
---|---|
11403-f-hoosa.mp4 | 5.76 MB |
Ƙara sabon ra'ayi