SHAHADAR SAYYIDA FADIMA (AS) (7)
Bayan Annabi (saw) ya daga hannun imam Ali (as) y ace: duk wanda na zamto shugabansa to Aliyyu shugabansa ne sai ya ce:
ya ku mutane wanda yake nan ya sanar wanda baya nan.
Kafin su watse sai Allah ya saukar da ayar yana cewa:
)اليوم أكملت لكم دينكم و أتممت عليكم نعمتي و رضيت لكم الإسلام دينا(
((A yau ne na cika muku addininku, kuma na cika ni’ima a gareku sannan na yardarmuku da musulunci shi ne addini gareku)
Sannan bayan saukar wannan aya sai dukansu suka yi ta yiwa Ali murna ta naɗashi halifan Manzon Allah (saww), daga cikinsu sahabban da suke a kan gaba wajan taya Imam Ali murna zama khalifan annabi akwai Abubakar da Umar har umar yake cewa bakkhin bakkhin laka wato farin cikin farin ciki gareka yau ka zama shugabana kuma shugaban dukkan wani mumini da mumina ya ɗan Abu Ɗalib.
Attachment | Size |
---|---|
11398-f-hoosa.mp4 | 30.09 MB |
Ƙara sabon ra'ayi