TARIHIN SAYYIDA FADIMA (AS) (2)
TSOKAR MUSƊAFA (SAWW).
Ku sani haƙiƙa it ce Faɗima shahida!
Tutar Ambato
Wannan Ambato ne da zukata suke kwankwasa saboda jinsa, zukata suke tsagewa yayin da suke tunaninsa saboda imani, zuciya tana yin godiya ga Allah saboda ya raya ta da tasirin tsananin kaunar Faɗima ta yi a cikinta, sannan zuciya tana wayar gari ta yammata tana mai kuka da baƙin cikin abin da ya faru a kan shugaba Nana Faɗima tsokr Manzo (saww) na kukan baƙin ciki, bacin rai, da kuma ƙunar zuciya tun daga ranar da mahaifinta ya bar duniya har ta koma ga rahamar ubangijinta.
Haihuwarta (as)
Ya zo a cikin littafin Dala'ilul Imama na Muhammad Ibn Jarir Aɗdabari Asshi'i shafi na 15 Abu Basir ya rawaito daga Imam Sadiƙ ya ce:
(An hafi Sayyida Faɗima a watan Jumada akhir ran ashirin daga cikinsa, shikara arba'in da biyar bayan haifar Annabi (saww), ta zauna a Makka shekara takwas, sannan ta zauna a Madina shekara goma, bayan wafatin mahaifinta kuma ta rayu kwana casa'in da biyar, ta yi shahada ranar talata uku ga watan Jumada Akhir a shekara ta goma sha ɗaya bayan hijira, Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareta, tare mahaifinta, da mahaifiyarta da mijinta, da ƴaƴanta)
Kunga an haifi Sayyda Zahra (as) shekara biyar bayan aiko Amnabi (saww) duk da cewa a kwai riwayoyi mabanbanta amma wannan shi ne zance mafi shahara.aa
Attachment | Size |
---|---|
11614-f-hoosa.mp4 | 36.77 MB |
Ƙara sabon ra'ayi