ALLAH YA KARE ALKUR’ANI DAGA TAHRIFI (6)

http://tvshia.com/file/0/11534-f-hoosa.mp4

Daga cikin abubuwan da ake ta yiwa makarantar Ahulul baiti(as) ƙazafi da shi su ne ana yi masu ƙazafi da cewa suna da alƙur’ani na su daban saɓanin wanda yake hannun sauran al’ummar bmusulmi, wani lokacin kuma ana yi musu ƙazafi da cewa suna da aƙidar cewa an canza Alƙur’ani ta hanyar shafe wasu ayoyi kamar ayar wilaya da makamantansu, don haka ne muke son mu yi bayani a kan waɗannan ƙaryace – ƙaryace don mutane su fahimci ƙaryane kuma yin imani da cewa wani zai iya sauya alƙur’ani ko kuma ta hanyar ƙara wani abu kokuma tauye wani abu ƙaryata Alƙur’ani ne, wannan bayani zai zo cikin mas’aloli kamar haka:

Kafin mu fara yin bayani a kan rashin yiwuwar tahrifi a ckin Alƙur’ani yana mutuƙar muhimmanci mu san mene ma’anar Tahrifi  a harshen larabci da kuma isɗilahi  kamar haka:

Ma’anar tahrifi a harshen larabci

Ta hrifi yana da ma’anar jan abu da kawar  da shi daga wajansa, asalin  wannan kalmar shi ne (حرف) (harf ) wato gefe idan aka ce: (حرف الشيء) ana nufin gefensa, irin wannan kalma da irin wanna ma’ana tazo a cikin   Alƙrur’ani inda Allah ya ke cewa:

 

{ وَمِنَ النَّاسِ مَن يَعْبُدُ الله عَلَى حَرْفٍ }

(Daga cikin mutane akwai masu bautawa Allah a bisa harafi )

wato suna yin bauta ne ba tsakani da Allah ba cikin zuciyarsu koda yaushe suna cikin cikin ruɗani ba sa cikin nutsuwa da addinin da suke , wato suna gefe sun raba ƙafa su ba su yi addinin tsakani da Allah ba su kuma basu bari ba.

AttachmentSize
File 11534-f-hoosa.mp429.75 MB

Ƙara sabon ra'ayi