TARIHIN SAYYIDA FADIMA (AS) (1)

Wannan Ambato ne da zukata suke kwankwasa saboda jinsa

TSOKAR MUSƊAFA (SAWW).

Ku sani  haƙiƙa it ce Faɗima shahida!

Tutar  Ambato

Wannan Ambato ne da zukata suke kwankwasa saboda jinsa, zukata suke tsagewa yayin da suke tunaninsa saboda imani, zuciya tana yin godiya ga Allah saboda ya raya ta da tasirin tsananin kaunar Faɗima ta yi a cikinta, sannan  zuciya tana wayar gari ta yammata  tana mai kuka da baƙin cikin abin da ya faru a kan shugaba Nana Faɗima tsokr Manzo (saww) na kukan baƙin ciki, bacin rai, da kuma ƙunar zuciya tun daga ranar da mahaifinta ya bar duniya har ta koma ga rahamar ubangijinta.

Haihuwarta (as)

Ya zo a cikin littafin Dala'ilul Imama na Muhammad Ibn Jarir Aɗdabari Asshi'i shafi na 15 Abu Basir ya rawaito daga Imam Sadiƙ ya ce:

(An hafi Sayyida Faɗima a watan Jumada akhir ran ashirin daga cikinsa, shikara arba'in da biyar bayan haifar Annabi (saww), ta zauna a Makka shekara takwas, sannan ta zauna a            Madina shekara goma, bayan wafatin mahaifinta kuma ta rayu kwana casa'in da biyar, ta yi shahada ranar talata  uku ga watan Jumada Akhir a shekara ta goma sha ɗaya bayan hijira, Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareta, tare mahaifinta, da mahaifiyarta da mijinta, da ƴaƴanta)

Kunga an haifi Sayyda Zahra (as) shekara biyar bayan aiko Amnabi (saww) duk da cewa a kwai riwayoyi mabanbanta amma wannan shi ne zance mafi shahara.aa

AttachmentSize
File 11613-f-hoosa.mp435.6 MB

Ƙara sabon ra'ayi