TARIHIN SAYYIDA FAƊIMA (AS) (19)
Sayyida Faɗima ta rayu tana maɗaukakiya, mai ladabi da kyawawan dabi'u, don haka jamaa da dama daga sahabbai kamar Khalifan farko da na biyu da wasu daga manyan ƙuraishawa suka nemi auranta, amma Annabi (saww) yana cewa: yana sauraron hukuncin Allah. Kamar yadda ya zo a cikin littafin Tazkiratul huffaz na Zahabi shafi na 306.
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ بُرَيْدَةَ، عَنْ أَبِيهِ رَضِيَ اللَّهُ Daga Buraida ya karɓo daga babansa ya ce: Abubakar da Umar sun nemi auren Faɗima sai Manzon Allah (saww) ya ce: ai ita karama ce, sai Ali ya nemi aurnta, sai ya aura masa ita. Wannan hadisin ingantacce ne a bisa sharaɗin Bukhari da Muslim amma ba su fitar da shi ba.
Wata rana Mala'ika Jibrilu ya sauka zuwa ga Annabi Muhammad (saww) yana mai bashi buhsara Allah yana umartarsa da ya aurawa haske haske, ma'ana ya aurar da Faɗima ga Ali(as).
Babban sahabin nan na Annabi (saww) Jabir ɗan Abdullahi ya rawaito cewa Annabi (saww) ya na cewa:
إنما انا بشر مثلكم‘ أتزوج فيكم وأزوجكم إلا فاطمة فإن تزويجها من الله نزل من السماء
(Haƙiƙa ni mutum ne kamarku ina yin aure a cikinku sannan ina aurar muku sai dai Faɗima kawai haƙiƙa aurenta daga sama Allah ya ɗaura shi sannan aka saukar da shi izuwa garemu).
An yi wannan aure na a cikin shekara ta biyu bayan hijira.
Sayyida Faɗima ta rayu a gidan mijinta rayuwa mai kyau cikin ladabi, ta kasance tana daka alkama kwaɓa ta da kanta ta yi gurasa. Allama Majlisi ya rawaito a cikin littafinsa Biharul Anwar juzi'I na 43 shafi na 50 cewa Imam Sadiƙ yana cewa:
Amirul Muminina Imam Ali (as) ya kasance yana yo itace, yana ɗebo ruwa kuma yana yin shara, ita kuma Faɗima (as) ta kasance tana nuƙa alkama, tana kwaɓa ƙulli, tana yin gurasa,)
Attachment | Size |
---|---|
12027-f-hoosa.mp4 | 40.15 MB |
Ƙara sabon ra'ayi