New York Times: Wasu Bayanan Sirri Na Danganta Saudiyya Da Harin 9/11
Jaridar ta ce tun a cikin watan da ya gabata ne ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Adel Jubair ya kai wata ziyara a Washington, inda ya sheda ma jami'an Amurka cewa, idan suka fallasa wadannan bayanai ta hanyar fitar da kudiri a Congress kan wannan batu, to Saudiyya za ta janye kudadenta da kaddarorinta da ke Amurka, wadanda suka kai kimanin dala biliyan 750, tun kafin a haramtawa Saudiyya taba su.
Wasu daga cikin 'yan majalisar dattijan Amurka sun bayyana cewa fitar da kudiri kan wannan batu zai yi mummunan tasiri a kyakyawar dangantakar da ke akwai tsakanin Amurka da Saudiyya, a kan haka suka yi kira da a sake yin nazari kan batun.
Daga cikin abin da bayanan sirrin suka kunsa dai a cewar jaridar New York Times, har da wata ganawa da ta gudana tsakanin wani babban jami'in diplomasiyyar kasar Saudiyya a Washington da wasu mutane biyu daga cikin wadanda suka kai harin 9/11 gab da lokacin da za su kai harin.
Ƙara sabon ra'ayi