Mutane 5 sun hallaka sakamakon tashin bom a kasar Somaliya
Kimanin Mutane 5 ne suka rasa rayukansu sannan kuma wasu 7 suka jikkata sanadiyar tashin wata Mota shake da bama-bama a gaban ofishin Gwamnatin kasar Somaliya dake birnin Magadushu.
Kamfanin dillancin Labaran France Press daga birnin Magadushu ya nakalto Abdul-fatah Umar Halanah kakakin Gwamnatin Somaliya na cewa daga mutane biyar din da harin ya ritsa da su na jiya Litinin a kwai kananen yara guda 2.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta daukin alhakin kai harin, sai dai ana zarkin kungiyar ta'addancin ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alqa'ida .
A bangare guda tawagar Majilisar dinkin duniya dake kasar ta yi alawadai da kai harin tare da bayyana shi a matsayin ta'addanci.
A shekarar 2014 kungiyar ta Ashaba ta mayaye manyan gariruwa da dama a kasar saidai a shekarar 2015 an fatattaki mayakan kungiyar daga manyan buranen kasar, inda yanzu haka abinda ya rake a hanun kungiyar bai fice wasu kauyuka ba daga tsakiya da kuma kudancin kasar.to saidai tun bayan da aka kwace manyan buranan kasar, kungiyar ta fadada kai hare-haren ta a manyan buranan, musaman ma birnin Magadushu, inda hedkotar Gwamnatin kasar ke can.
Ƙara sabon ra'ayi