Jami'an Tsaron Guinea Conakry Sun Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar
Jami'an tsaro a Guinea Conakry sun dauki matakin tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar da nufin dakile duk wani shirin kai harin ta'addanci musamman bayan hare-haren ta'addancin da aka kai kasashen Mali da Ivory Coast.
Ministan tsaron kasar Guinea Conakry Kebele Camara ya sanar da cewa: Gwamnatin kasarsa ta samar da wata rundunar tsaro ta musamman da zata dauki nauyin fada da ta'addanci a kasar.
Kebele Camara ya kara da cewa: Rundunar tsaron ta musamman ta hada da 'yan sanda, Jandamari da sojoji kuma tana cikin shirin kalubalantar duk wata barazanar tsaro a kasar musamman ayyukan ta'addanci.
Mahukunta a kasar ta Guinea Conakry sun hanzarta daukan wannan mataki ne domin zaman cikin shirin kalubalantar duk wani harin ta'addanci da za a kaddamar kan kasar musamman ganin yadda aka kai hare-haren ta'addanci a kasashen Mali da Ivory Coast da suke makobtaka da kasar ta Guinea Conakry.
Ƙara sabon ra'ayi