An kashe Sojojin hayar Saudi-arabia da dama a Yemen
Majiyar Labaran kasar Yemen ta sanar da hallaka wani adadi mai yawa daga cikin sojojin hayar Saudiya a jihohin Ta'az da Baida'a na kasar Yemen.
Kamfanin daillancin Labaran kasar Yemen Saba ya habarta cewa A jiya Litinin Sojoji da Dakarun sa kai na kasar sun hallaka Sojojin hayar masarautar Ali-saaoud da dama a yayin wani hari da suka kaiwa tankokinsu a jihar Ta'az dake kudu maso yammacin kasar.
Har ila yau a garin Zahir dake jihar Baida'a a kudancin yemen din, Dakarun tsaron kasar tare da na sa kai sun samu nasarar dakile ci gaban da Sojojin hayar Saudiyar kai yi a yankin tare kuma da hallaka wani adadi mai yawa daga cikinsu.
Ƙara sabon ra'ayi