An hallaka 'yan ta'addar IS da dama a Dairi zur na kasar Siriya

Sama da 'yan ta'addar ISiS 40 ne aka hallaka a jihar Dairu zur dake gabashin kasar Siriya

 

 

Kamfanin dillancin labaran Sana na kasar Siriya ya habarta cewa a wannan Assabar jiragen saman yakin kasar sun yi lugudar wuta kan maboyar 'yan ta'addar ISIS dake gefen gabashin Dairu Zur, inda suka hallaka 'yan ta'adda sama da 40 tare da lalata na'urorinsu da dama.

Har ila yau jiragen saman yakin na kasar Siriya sun yi ruwan bama-bamai a gurin taruwar 'yan ta'addar ISIS dake filin sauka da tashi na jiragen saman Attabaka dake gefen yammacin garin Rikka , shi dai wannan gari na Rikka dake arewa maso gabshin Siriyanr na a matsayin babbar tungar 'yan ta'addar ISIS a kasar.

A daren juma'a da ta gabata ma Dakarun tsaron sa kai na Siriya sun hallaka 'yan ta'addar ISIS sama da 30 a garin Muhsin.

Tun bayan 'yanto garin Tadmur mai dunbin tarihi dake jihar Humus, Sojojin na Siriya sun kara samun karfin gwiwa wajen ci gaba da yakar 'yan ta'addar na ISiS.

Bayan tabka kazamin fada na kwana da kwanaki tsakanin Dakarun tsaron kasar da mayakan ISIS, a ranar 27 ga watan Maris din da ya gabata aka ceto garin Tadmur wanda yake hanun 'yan ta'addar tun a watan Mayun shekarar 2015 din da ta gabata.

Ƙara sabon ra'ayi