MDD ta yi alawadai kan harin da aka kaiwa Dakarun sulhu na Majalisar a yankin Darfur

Babban Saktaren MDD ya yi alawadai kan harin da aka kaiwa Dakarun sulhu na Majalisar a yankin Darfur na kasar Sudan

 

 

Kamfanin dillancin Labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto Banki Moon babban sakataren MDD da Nkusazana Delemi Zuma shugaban kwamitin kungiyar Tarayar Afirka cikin wani bayyanin hadin gwiwa da suka fitar jiya Alkhamis,suna Alawadai da harin da aka kaiwa Dakarun tsaro da Sulhu na MDD da aka baiwa suna Younamid a yankin Darfur, sannan su bukaci magabatan Sudan da su gudanar da bincike domin kame wadanda suka kai wannann hari tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

wannan harin dai an kai shi a yayin da dakarun sulhun na MDD ke bada kariya ga wata tawagar kai agaji a yankin na Darfur, ranar Larabar da ta gabata, inda aka kashe Jami'an Dakrun guda na kasar Sudan ta kudu tare kuma da jikkata wani na daban.

A jiya Alkhamis ma Kwamitin tsaro na MDD ya yi alawadai da wannan hari, inda ya bayyana shi a matsayin Laifin yaki.

Ƙara sabon ra'ayi