Sakamakon Zaben Kasar Benin
An sanar da sakamakon zaben shugaban kasar Benin.
Jaridar Lo figaro ta faransa ta buga a shafinta na internet cewa; Sakamakon zaben da aka sanar a kasar Benin na nuni da cewa; Pira minista Lionel Zinsou ne ya ke kan gaba da kuriu dubu dari 856 ( 28%) na jumillar kuri'un da aka kada. Mutum na biyu da ya ke binsa shi ne Ptrice Talon wanda ya sami kuri'u dubu dari 746 ( 24%) na kuri'un da aka kada.
Hukumar zaben kasar ta Benin ta sanar da cewa; saboda la'akari da cewa babu daya daga cikin 'yan takarar da ya lashe zaben, za a je zagaye na biyu a tsakanin wanda ya zo na daya da na biyu. 'Yan takara 33 ne su ka yi gogayya da juna a zaben da aka yi a kasar ta Benin.
Ƙara sabon ra'ayi