Gwamnati: "Shigar Nijeriya Kawancen Musulunci Ba Shi Da Alaka Da Addini"

Ministan harkokin wajen Nijeriya Mr. Geoffrey Onyama ya bayyana cewar sabanin korafe-korafen da wasu suke yi, shigar Nijeriya rundunar hadin gwiwar kasashen Musulmi karkashin jagorancin Saudiyya don 'fada da ta’addanci' ba shi da alaka da wani addini.

 

 

Jaridar Leadership ta Nijeriyar ta bayyana cewar ministan harkokin wajen na Nijeriya ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a fadar mulkin kasar a Abuja inda ya ce ta'addanci dai wani lamari ne da addabi duniya don haka Nijeriya a shirye take ta goyi bayan duk wani yunkuri na ganin bayansa.

Minista Onyama har ila yau yayi kakkausar suka ga wasu kafafen watsa labarai wanda yace suna kokarin murguda hakikanin lamarin inda ya ce maimakon su yi hakan kamata yayi su yi bayanin hakikanin manufar hadin gwiwar, yana mai cewa hadin gwiwan wani kokari ne na kasashen musulmi na nuna cewa ta'addanci dai ba shi da wata alaka da addinin Musulunci.

A shekaran jiya ne shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari, a wata hira da yayi da tashar talabijin din Al Jazeerah, ya ce Nijeriya za ta shiga cikin rundunar hadin gwiwar kasashen Musulmin karkashin Saudi Arabia da nufin fada da ta’addanci, saboda kuwa Nijeriyar na fama da bala’in ‘yan ta’addan da ke ikirarin suna da alaka da addinin Musulunci yana mai ishara da kungiyar Boko Haram da take ci gaba da zubar da jinin al'ummar kasar.

Ƙara sabon ra'ayi