Wani Bom Ya Tashi A Filin Jirgin Saman Garin Baidawin Na Kasar Somaliya

Tashin bom a filin jirgin saman garin Baidawin na kasar Somaliya ya yi sanadiyyar jikkata mutane akalla shida kuma biyu daga cikinsu jami'an tsaron kasar.

 

 

Kamfanin dillancin labaran France Press ya habarto daga majiyar tsaron Somaliya cewa; Wani bom da aka dana a cikin kwamfuta ya tarwatse a farfajiyar gudanar da binciken kayayyakin matafiya a filin jirgin saman garin Baidawin na Somaliya lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatan mutane shida, biyu daga cikinsu jami'an tsaro ne da suke kula da tsaron filin jirgin.

 

A bayan tashin bom din jami'an tsaron Somaliya sun tsananta gudanar da bincike lamarin da ya kai su ga gano wasu bama-bamai biyu na daban, kuma sun yi nasarar lalata su kafin fashewarsu.

Ƙara sabon ra'ayi