An Kama Wani Mai Samarwa Boko Haram Makamai a Nigeria

Gwamnatin Nigeria ta bada labarin cewa jami'an tsaron kasar ta kama

 

 

Gwamnatin Nigeria ta bada labarin cewa jami'an tsaron kasar ta kama wani mutum wanda yake samarwa kungiyan nan ta yan ta'adda a kasar wato Boko Haram. Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto kakakin jami'an tsaro ta DSS Tony Opuiyo yana fadar haka a jiya Lahadi. Ya kuma kara da caeawa DSS ta kama Musa Garba Abubakar ne a birnin Jos babban birnin Jihar Plator kuma sun sami makamai da dama a wajensa wadanda suka hada da Cartridge 80 na albarusai da wasu nau'in makaman. Banda haka Opuiyo ya kara da cewa an kama wasu abokan aikinsa a wannan bangaren inda a halin yanzu ake ci gaba da bincikensu.

Tun shekara ta 2009 kungiyar Boko Haram ta fara daukar makami a arewacin tarayyar Nigeria inda suka kashe fiye da mutane dubu 17 wasu miliyoyi kuma suka kaura cewa gidajensu.

Ƙara sabon ra'ayi