Kungiyoyi Da Dama Sun Yi Allah Wadai Da Sanya Hizbullah Cikin Yan Ta'adda

Wasu kungiyoyi da dama a kasar Masar sun yi All.. wadai da kasashen larabawa

 

 

Wasu kungiyoyi da dama a kasar Masar sun yi All.. wadai da kasashen larabawa na yankin tekun farisa wadanda suka sanya kungiyar Huzbullah cikin jerin kungiyoyin yan ta'adda a duniya.

Tashar televisin ta Al-Akhabar ta nakalto Khalid Al-Kilani wani daga cikin fitattun yan jarida a kasar Masar yana bayyana cewa kasashen larabawa na yankin tekun farisa musamman kasar Saudia suna sun raba kan kasashen larabawa ne da matakin da suka dauka na sanya kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon a cikin jerin kungiyoyin yan ta'adda.

Hakama Mahmood Askalani na kungiyar yan jaridu ta حزب عربی ناصری ya yi kira ga kasashen larabawa su yi watsi da matsayin da kasashen larabawa na yankin tekun farisa suka dayka na son maida hizbulah saniyar ware. Ya kuma kara da cewa kungiyar Hizbulla da kuma kungiyoyi masu gwagwarmaya ne kadai suke iya samun nasara kan HKI a yankin don haka ne kasashen Larabawa suke son maida ita saniyar ware.

Ƙara sabon ra'ayi