Tashar Telbijin din Faransa ta sanar da cewa; kawo ya zuwa yanzu Kungiyar Bokoharam ta sace kananan yara fiye da dubu 800 a cikin Najeirya kadai.
Rahoton na Tashar Telbijin din Farance Info ya ci gaba da cewa da akwai wasu dubban kananan yaran da kungiyar ta bokoharam ta raba su da iyayensu, tare da tilastawa wasunsu yin aure.
Rahoton Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unucef ya ambaci cewa; A cikin shekara guda kadai adadin yaran da kungiyar ta bokoharam ta cutar da su ya rubanya.
Asusun na kananan yara, ya kuma bayyana cewa adadin makarantun da aka rusako lalatawa ko kuma daina yin karatu a cikinsu, sun haura dubu daya da dari daya.
Ƙara sabon ra'ayi