Kasashen Larabawa Sun Yi Allawadai Da Bukatar Turai Ta Hana Sayarwa Saudia Makamai
Majalisar kasashen Larabawa ta yi All...wadai da shawarar da majalisar tarayyar Turai
Majalisar kasashen Larabawa ta yi All...wadai da shawarar da majalisar tarayyar Turai ta yanke na yin kira ga kasashen yankin su daina sayarwa kasar Saudia makamai. Tashar television ta Al-Masir ta Ahmad bin Mohammad Jarwan shugaban majalisarb dokokin kasashen Larabawa yana fadar haka a jiya, ya kuma yi kira ga majalisar tarayyar ta Turai ta sake nazarin matsayin da ta nauka na yin kira ga kasashen Turai su daina sayarwa saudai makamai.
A ranar Alhamis da ta gabata ce majalisar ta Turai ta kada kuri'a kan hana sayarwa saudia makamai inda wakila 212 suka amince da hakan a cikin wakilai 359. A yayinsa wakilai 31 suka ki kada kuri'unsu.
Tun watan Maris shekara ta 2015 ne kasar Saudai da kawayenta suka fara kai hare hare kan kasar Yemen, inda dubban mutanen kasar, hada da mata da yara suka rasa rayukansu.
Ƙara sabon ra'ayi