Kwamandan lardin Anbar da ke yammacin kasar Iraki Isma'il Mahlawi ya sanar da cewa; A samamen da sojojin gwamnatin Iraki suka gudanar da yankuna daban daban da suke lardin Anbar musamman a yankin Ha'midiyya, Bouziyab, Bouda'iyj da yankin Salam sun yi nasarar kashe 'yan ta'addan kungiyar Da'ish 64.
Har ila yau sojojin gwamnatin Iraki sun samu nasarar lalata bama-bamai fiye da 100 a yankunan da suka gudanar da samamen a jiya Litinin. Kamar yadda sojojin na Iraki suna samu nasarar tarwatsa rumbun tsimin man fetur da 'yan ta'addan kungiyar Da'ish suke amfani da shi a garin Ramadi da ke lardin na Anbar.
Ƙara sabon ra'ayi