Gambiya : Yahya Jammeh Zai Yi Takara A Karo Na Biyar
Jam'iyyar (APRC) mai mulki a kasar Gambiya ta sake tsaida shugaban kasar Yahya Jammeh wanda ya shafe shekaru 21 kan madafun iko a matsayin dan takara ta a zaben shugaban kasar na watan Disamba.
Mr. Jammeh wanda ya kama mulki a wannan kasa bayan wani juyin mulki a shekara 1994 na neman wani wa'adi ne a karo na biyar.
Shi dai shugaba Jammeh mai shekaru 50 da haihuwa da ke jan ragamar wannan karamar kasa da ke a Yammacin Afirka ana masa kallo na dan kama karya.
Kasar ta Gambiya me alumma kimanin miliyan biyu kashi casa'in cikin dari na zama Musulmi yayin da kashi takwas cikin dari ke zama Kirista kashi biyu kuma masu bin addinin gargajiya. shugaban kasar Jammeh na shan sukar 'yan fafutika da kasashen Yamma ko da a shekarar 2010 sai da kungiyar EU ta tsaida tallafin Euro miliyan 22 da za ta ba wa kasar saboda batutuwa da suka shafi take hakkin bil Adama.
Ƙara sabon ra'ayi